1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita kan barazanar ISIS a Arewacin Afirka

July 8, 2014

Jami'an leken asirin kasashen Masar da Tunusia da Aljeriya sun gudanar da taro don tunkarar matsalar bullar reshen mayakan ISIS a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/1CYBn
ISIS Kämpfer Militärparade in Syrien 30.06.2014
Hoto: Reuters

Ministan cikin gidanTunisia Mun ji Hamidi, ya ba da sanarwar cewar ranar 13 ga wannan watan da muke ciki ne, ministocin waje na kasashen da ke makwabtaka da Libiya za su hadu a Tunisiya don tattauna batun barazanar tsaron da kungiyoyin masu dauke da makamai za su iya yi a yankin, musamman bayan da jami'an leken asirin kasashen da suka gama ganawa a wannan Litinin, suka bada tabbacin bullar kungiyar ISIS mai fafutukar kafa daular musulunci a kasar ta Libiya.

Ahmad Wanees, tsohon ministan harkokin wajen kasar ta Tunisia, daya daga cikin wadanda suka gudanar da zama kan duba yadda za'a tunkari abin daya kira "Annobar da ke yaduwa kamar wutar daji" ya ce kalubalen bullar kungiyar ta ISIS a kasar Libiya, batu ne da ya zama wajibi a yi taron dangi don dakatar da shi.

Bayan da kungiyar ta ISIS da ke neman hade illahirin kasashen Larabawa karkashin tuta daya, ta samu gindin zama a kasar Iraki, kamar yadda bayanan asirai na kasa da kasa ke tabbatarwa, kungiyar ta tura wakilanta da take kira Umara'u zuwa kasashen, cikin har da kasar Libiya da take da dimbin mabiya cikinta.

Bayanan asiri da kwararru kan tsaro na kasashen ke tattunawa dai sun hada da yunkurin gwara kan kungiyar ta ISIS ta takwararta ta Alka'ida, wadanda a yanzu haka, suke zaman doya da manja sai dai masanan na kashedin cewa, hakan kan iya zama shuka a idon makwarwa.

Mawallafiya: Mahmud Yaya Azare
Edita : Zainab Mohammed Abubakar