1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba wa kungiyar AU

Zulaiha Abubakar MNA
February 9, 2019

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana gudanar da zabuka lafiya da kuma kawo karshen rikici a wasu kasashen Afirka da alamu na nahiyar ta fara zama abin misali ga sauran kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/3D3B6
Genf Geberkonferenz Jemen
Hoto: Reuters/P. Albouy

A yayin da ya sauka kasar Habasha don halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka AU, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya kara da jinjina wa kasashen Eritiriya da Habasha da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bisa sulhun da ya tabbata a kasashen tare da fatan ganin kasar Libiya za ta yi koyi.

A baya al'ummar kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Mali da Madagaska sun yi hasashen barkewar rikici bayan zabubbukan kasashen, amma a karshe sun gudana ba tare da mummunar tarzoma ba.

Magatakardan ya kuma jinjina wa Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar AU bisa kokarinsu na kawo dorewar zaman lafiya a wasu yankunan na Afirka.