1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magoya bayan Mursi na Zanga-zanga

August 30, 2013

Magoya bayan jami'iyyar 'yan uwa Musulmi a Masar sun yi watsi da gargadin mahukuntan kasar inda suka bazama kan titunan kasar don gudanar da zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/19Z77
epa03811057 Supporters of ousted President Mohamed Morsi protest near Rabaa Adawiya mosque after Friday prayer in Cairo, Egypt, 02 August 2013. Egyptian police on 01 August called on backers of ousted Islamist president Mohammed Morsi to end sit-ins in two Cairo areas signalling an imminent security crackdown upon the large protests.The Interior Ministry which is in charge of security forces said it had started taking necessary measures to end the vigils in the area of Rabaa al-Adawiya in eastern Cairo and al-Nahda Square south of the capital EPA/KHALED ELFIQI
Ägypten Mursi Anhänger Kairo 02.08.2013Hoto: picture-alliance/dpa

Masu aiko da rahotanni sun ce an fara zanga-zangar ce bayan kammala sallar Juma'a a birnin Alkahira da Isma'iliya da sauaran bangarori daban-daban na kasar, inda suke ta rera kalamai na kin jinin sabbin mahukuntan kasar.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Masar din ta ce ta girke jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana a wurare daban-daban na Alkahira da sauran yankunan kasar.

A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun bude wuta kan wani ofishin 'yan sanda a yankin Heliopolis da ke birnin Alkahira da safiyar yau, inda dan sanda guda ya ransa ransa.

Kamfanin dillancin labaran Masar na MENA wanda ya rawaito wannan labarin ya ce baya ga dan sanda da ya rasu, wasu karin mutane ciki har da fara hula sun jikkata a harin wanda ba a san musbbabin kai shi ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu