Mahaukaciyar guguwa ta ratsa arewacin Jamus

Mutane shida ne suka mutu sakamakon faduwar bishiyoyi yayin da wata mahaukaciyar guguwa ta ratsa yankin Arewacin da kuma Gabashin Jamus inda ta haddasa dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa.

A birnin Hamburg da ke arewacin kasar wata uwar itaciya ta fada kan wata mota da ke dauke da wasu mata biyu, inda daya daga cikinsu ta mutu ya yin da dayar ke a asibiti a cewar jami'an 'yan sanda. Shi ma wani direba ya mutu sakamakon faduwar wata uwar bishiya a cikin jihar Mecklenburg-Vorpommern, yayin da a jihar Brandebourg da ke kewaye da birnin Berlin, nan ma wata mata ta mutu sakamakon yadda wata katuwar bishiya ta fada wa motarta, yayin da shi ma wani da ke cikin motarsa a wannan yanki ya rasu sakamakon wani rehen itaciya da ya fada wa motarsa.

An dakatar da dukannin zirga-zirgar jiragen kasa a yankin arewacin kasar ta Jamus, musamman ma babban hanya daga Hamburg zuwa birnin Berlin, sannan kuma da wani yanki na gabashin kasar a cewar babban kamfanin zirga-zirgar jiragen kasan na Jamus na Deutsche Bahn. Jami'an kwana-kwana sun aiwatar da ayyukan ceto fiye da 800 bayan da jama'a ke kiransu domin kawo musu dauki. Mugunyar guguwar mai suna Xavier na gudun da ya kai na kilo mita 120 zuwa 140 a sa'a daya.

 

Ƙarin rahotanni

Rahotanni masu dangantaka