1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahaura ƙarshe a taron G8

June 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuJU

Yau ne rana ta 3 kuma ta ƙarshe, a taron shugabanin ƙasashen ƙungiyar G8 da ke ci gaba da wakana a birnin Heiligendamm na ƙasar Jamus.

A wani mataki na ba zata, ƙasashen, sun cimma daidaito a game da batu mai sarƙƙaƙiya, na yaƙi da ɗumamar yanayi.

Mahaurorin da za su gudanarwa a yau, sun jiɓacin taimakon raya ƙasa da ƙungiyar ke baiwa nahiyar Afrika a yunƙurin ta na yaƙi da talauci.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angeller Merkel ta alkawarta shigewa Afrika gaba, a taron domin ƙara bunƙasa tallafin da G8 ke baiwa wannan nahiya.

Taron zai saurari wakilan Afrika da su ka haɗa da shugaban ƙasar Ghana, John Kuffor, bugu da ƙari shugaban ƙungiyar taraya Afrika, da kuma shugaban ƙasar Nigeria, Al haji Umaru Musa Yar Aduwa.

Saidai a ɗaya hanun, tawagogi da ƙasashe daban-daban na dunia na gudanar da nasu taro a ƙasar Mali, da su ka raɗawa suna „taron ƙasashen yan rabana ka wadata mu“, sun ce G8 ba za ta iya tsinan komai ba,a game da batun yaƙi da talauci a ƙasashe masu tasowa.