1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan kamen 'yan PDP a badakalar makamai

Ubale Musa/GATDecember 2, 2015

A Najeriya kasa da 'yan awayoyi da kamen wasu 'ya'yan jam’iyyar PDP ta adawa a bisa zargin hannu a cikin badakala ta makamai, mahawara ta kaure a tsakanin masu tunanin an yi dai-dai da kuma masu kallon akasin haka.

https://p.dw.com/p/1HG6r
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Kasa da 'yan awayoyi da kamen wasu 'ya'yan jam’iyyar PDP ta adawa a bisa zargin hannu a cikin badakala ta makamai, mahawara ta kaure a tsakanin masu tunanin an yi dai-dai da kuma masu kallon da akwai matsala a cikin tsarin

Babu dai ko da guda a cikinsu dake da tarihi na shiga aikin soja, sannan kuma ba’a sansu da a sunan dillallai na makamai ba, to sai dai kuma sun dau kasar cikin mamaki bayan da hukumar yaki da halatta haramun din EFCC ta gaiyyaci wasu 'ya'yan jam’iyyar PDP ta adawa guda uku kuma ta tsare.

EFCC dai ta ce Alhaji Bashir Yuguda, da kuma High Chief Raymond Dokpesi sannan da Attahiru Dalhatu Bafarawa na da abun fada cikin badakalar sayen makaman kasar da iskarta ke kadawa cikin kasar a halin yanzu.

Biliyoyin nairori ne ake fadin sun saka hannu sun kuma karba daga offishin tsohon mashawarcin tsaron kasar Kanal Sambo Dasuki, sannan kuma babu bayanin bahasinsu a bangare na jami’an.

Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan in Brüssels
Hoto: picture-alliance/dpa

Ana dai zargin karkartar da biliyoyi na kamfen din yaki na ta’addancin cikin kasar ya zuwa yakin neman arcewar shugaba Goodluck Ebele Jonathan din da ya kare ba nasara.

Sannu a hankali dai offishin tsohon babban jami’in tsaron da ke da alhaki da tabbatar da kai karshen annobar ta haramun ya koma hedikwatar rabon kudi na neman sai ta zarcen ta Jonathan

Abin kuma da ya kai ga bacewar duban miliyoyin nairori dama dalolin da aka ce an ware da nufin samar da makaman yaki amma kuma sun kare a cikin aljihu na kalilan.

Duk da cewar dai babu dalla dalllar rawa ta kowa a bangaren EFCC a tunanin Dr Umar Ardo wani dan jam’iyyar PDP da ya kalli yanda tsarin zaben ya tafi to ko akwai kwarara na kamanni a tsakanin birin da ke lilo a sama da kuma mutumin da ke tafiya a kan kasa cikin tunkaho.

To sai dai komai nisa na kamannin dan juma da dan uwansa dan jumai dai, a tunanin jam’iyyar PDP da ko bayan guda ukun dake zaman 'ya'yanta na hudunsu kuma da yanzu ya aro 'yar buya ke zaman shugaban kwamiti na amintattunta, akwai bukatar taka tsantsan a bangaren EFCC da ke zaman hukuma ta binciken 'yan laifi ba alkali ba.

Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kakakin jam’iyyar Olisah Metuh dai ya ce sakonnin da ke fitowa daga hedikwata ta hukumar na neman wuce gona da iri a cikin Najeriyar da kowa ke da 'yanci har sai an tabbatar da laifi kansa.

"Dokpesi ba shi da laifi haka ma ragowar, sai ka kai ga shari’a ta mutane kake iya yanke hukunci kansu. Kalaman EFCC na nunin cewar an same su da laifi. In haka ne me ya sa kake batun alkali. Ko kuma sun koma masu bincike da yanke hukunci. In haka ne ba mu bukatar alkali. Mutanen dake bincike sun yanke hukunci kan wadanda suke bincike a kansu. Kuma a inda aka kai karatun an waye to hakan yana nufin cin zarafi. Ba mu son yanke hukuncin cewar ana bin mutanen da suka taka rawa a cikin yakin neman zabenmu musamman ma ga batun Dokpesi, amma dai muna kuma taka tsantsan."

Tuni dai tarun 'yan kamen ke kara cika da masu ruwa da tsaki da badakalar da ta tada hankali ciki da ma wajen kasar.

Na baya-baya na zaman tsohon mashawarcin tsaron kasar a farko na gwamnatin ta Jonathan kuma tsohon shugaban hukumar asiri ta cikin gida ta SSS da aka cafke a Iko da ranar wannan Laraba