1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan matsalolin tsaron Najeriya

November 14, 2013

Batutuwa na cigaba da tasowa dangane da sanya ƙungiyoyin Boko Haram da Ansaru a jerin ƙungiyoyin ta'addanci da Amirka ta yi, inda manazarta ke nazarin tasirin da hakan zai yi ga ƙasar

https://p.dw.com/p/1AHhf
A Joint Military Task Force (JTF) soldier positions his rifle on sand bags on the road in northeastern Nigerian town of Maiduguri, Borno State , on April 30, 2013. Fierce fighting between Nigerian troops and suspected Islamist insurgents, Boko Haram at Baga town in the restive northeastern Nigeria, on April 30, 2013 left dozens of people dead and scores of civilians injured. But the military denied the casualty figures claiming it was exaggerated to smear its image. Meanwhile normalcy has return to the town as residents are going about their normal business. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Amirka ta sanya ƙungiyoyin Boko Haram da Ansaru waɗanda ke fafutukan ganin Najeriya ta yi amfani da dokokin musulunci a ƙasar, cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda, kuma ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta bayyana cewa wannan matakin ya zama tilas ne domin taimakawa Najeriya wajen daƙile irin rikice-rikicen da suka addabe ta, to sai dai wannan na nufin cewa hukumomin sa idon Amirka na da ikon hana waɗannan ƙungiyoyi shiga hulɗoɗin cinikayya da kasuwanci da sauran ƙungiyoyi ko hukumomin ƙasashen ƙetare.

To ko ta yaya wannan mataki zai yi tasiri kan Najeriyar a daidai wannan lokaci?

A wata sanarwar da ta fitar gwamnatin Amirka ta ce wannan mataki ya zama wajibi kuma wannan ne irin matakin da Najeriya ke buƙata idan har tana so ta sami maslaha mai ɗorewa to ko me sanya waɗannan ƙungiyoyi bisa jerin ƙungiyoyin ta'addancin ke nufi? shin tana da hurumin shiga Najeriya ke nan, ko kuma ma ta yi amfani da jirage marasa matuƙa kamar yadda take yi a Pakistan? Major Yahaya Ibrahim Shinku mai retaya ƙwararre ne kan tsaro kuma ya yi mana ƙarin bayani

"Ita Amirka a nata tsarin to ko ina wannan ƙungiya take za ta yake ta, za ta bi ta har inda take ba sai ta bari da zo ƙasarta ta ishe ta ba, daga ƙarshe irin abubuwan da za su fara faruwa ke nan, ko da kai tsaye basu fara kawo waɗannan jiragen ba, za su fara bin hanyoyin da za su ga zasu taimakwa Najeriya ta yaƙe ƙungiyar idan aka ga kaman ta gaza kamar yadda muke gani yanzu."

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Shugaban ƙungiyar Boko Haram Imam Abubakar ShekauHoto: AP

Yunƙurin kiran Boko Haram ƙungiyar ta'addanci a baya

A baya wasu ƙungiyoyi sun taɓa gabatar da buƙatar sanya Boko Haram a jerin irin waɗannan ƙungiyoyi amma kuma sai ta ɗebi mutane uku ta kuma ware kyautar kuɗin da ta yi alƙawarin baiwa duk wani wanda ya miƙa su, wannan dai ya sanya tambayar abin da ya sauya kawo wannan lokaci, abin da kuma mahukuntan Amirkan suka kare kansu suna cewa a baya sun zata ƙungiyar ba ta da wata barazana ga ƙasashe irin na su, wato ƙarfinta a cikin gida ya tsaya amma kuma a shekaru ukun da suka gabata sun ga cewa dangantakarta ya faɗaɗa zuwa ƙasashen waje.

Yanzu da wannan mataki, wani alfanu ne Najeriyar za ta samu, za a yi mata ƙarin tallafi ne? Major Yahaya ibrahim Shinku na ganin shakka babu

"Za ta ƙara mata kuɗin tallafi tun da yanzu ƙungiyar ta zama ta 'yan ta'adda, duniya gaba ɗaya ta yi Allah wadai da ita, kuma sun haɗa gwiwa da ita zasu yaƙe ta, musamman yanzu tunda zata kasance ƙarƙashin dokar yaƙi da ta'addanci ta duniya, Amirka za ta fake ta yi duk abin da ta ga ya kamata"

PRESIDENT GOODLUCK JONATHAN (5TH L) ; VICE-PRESIDENT NAMADI SAMBO (6TH L) WITH MEMBERS OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH AFTER THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13).
Kwamitin shugaban ƙasa na shiga tsakanin gwamnati da Boko HaramHoto: DW/A. Ubale Musa

Ra'ayoyi dangane da ƙara wa'adin dokar ta ɓaci

Mohammed Mustapha Yahaya daga ƙungiyar tabbatar da wanzara da demokraɗiyya ta ƙasa da ke Kano wadda ake kira Democratic Action Group ya ce kamata yayi a gudanar da wasu sauye-sauye idan har ana so dokar ta yi aiki

"Yaya za'a yi a baiwa dokar abin da ake kira "Human face" ya zama cewa akwai kula da hakkin ɗan adam, kuma a ce jami'an tsaro na aiki hannu da hannu, kafaɗa da kafaɗa da su da jama'a. Ɗaya daga cikin matsalolin dai da nake gani ita ce katse kafofin sadarwa, idan aka kai hari a wani ƙauye babu yadda za a yi su sanar da jami'an tsaro"

Sai dai masanin tsaron Yahaya Ibrahim Shinku ya ce gaba ɗaya ya kamata ma a sauya salo.

Yunƙurin Majalisun ƙasar wajen daidaita matsalar

"Yadda 'yan majalisar tsaro suka yi suka ce sai jami'an tsaro sun zo sun basu hujjoji sun dace, dan su ne suka baiwa shugaban ƙasa shawarar cewa idan aka basu dama za su shawo kan wannan matsalar, daga lokacin da aka basu wannan dama zuwa yanzu, abubuwa sun taɓarɓare, domin ya nuna cewa sojojin Najeriya sun gaza

Haka nan kuma wata matsala da ake dangantawa da koma bayan da ake cigaba da samu ita rashin aiwatar da rahotannin da kwamitoci suka bayar, da ma rashin bayyanawa al'uma duk abubuwan da rahotanni suka ƙunsa musamman wanda ya shafi shiga tsakanin gwamnati da Boko Haram, inda masu fashin baƙi ke zargin cewa kanun rahoton ne kaɗai aka bayyanawa al'umma.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba

Edita: Saleh Umar Saleh