1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da MuhalliAfirka

A birnin Abuja na Najeriya an hana zanga-zangar kare muhalli

Uwais Abubakar Idris SB
March 19, 2021

‘Yan sanda a Najeriya sun hana zanga-zangar neman mahukunta su dauki mataki a kan matsalar sauyin yanayi wadda ake yi domin jawo hankalin hukumomi su dauki mataki.

https://p.dw.com/p/3qs8M
Nigeria Abuja | Klimastreik: Fridays for Future
Hoto: DW/W. Abubakar Idris

Tun da sanyi safiya ne dai ‘yan sandan Najeriyar suka yi kawanya tare da toshe dandalin ‘yancin wurin da masu zanga-zangar suka shirya hallara domin gudanar  maci na lumana domin wannan rana. Birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya ya kamata ya bi sahun sauran birane 50 na duniya da ake wannan zanga-zangar neman daukan mataki a kan tabarbarewar sauyin yanayi a duniya da yadda take shafar muhallin da bani adama ke rayuwa a cikinsa. Isiah Nuhu I Isiyaka.

Sanin cewa Najeriyar na cikin kasashen da ke da dimbin matsaloli na gurbacewar mahalli kama daga gurgusowar Hamada zuwa ga zaizayar kasa da gurbata muhalli a dalin aiyyukan hako mai a yankin Niger Delta lisafi ne mai tsawo na matsalolin da kasar ke fuskanta. Ko wace illa hana gangamin na jawo hankalin mahukuntan kasar da a mafi yawan lokuta alkawuran daukan mataki a fatara baka yake karewa zai yi? Mr Oluwasemiye Micahel shine shugaban kungiyar Dean initiative ta masu  rajin kare muhalli a Najeriyar wanda ya nuna rashin jin dadi da matakan hana takura musu.

Nigeria Abuja | Klimastreik: Fridays for Future
Hoto: DW/W. Abubakar Idris

Masu rajin kare hakin jama'a dai sun dade suna nuna ‘yar yatsa a kan ikon da mahukunta ke da shin a hana duk wata zanga-zanga domin yanci ne na dan kasa. Barrister Mainasara Umar masani ne a fanin shari'a a Najeriyar.

Duk da wannan haramci ga IIsiah Nuhu Isiyaku  mai rajin a kawo karshen matsalar sauyin yanayi a Najeriyar ya bayyana sakonsu a wannan rana.

A yayin da birane 50 na duniya ke gangami na neman a dauki mataki kan matsalar sauyin yanayi, lamari ne da ke kara zama zahiri ga rayuwar bani adama kama daga karuwar matsanacin zafi dalilin dumamar duniya ya zuwa ambaliyar ruwa da gurbacewar mihalli a yankin Niger Delta.