1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukuntan Najeriya sun lashe amansu

Ubale MusaNovember 5, 2014

Mahukuntan Tarayyar Najeriya da suka ce sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Boko Haram makwanni kusan biyu da suka gabata, sun ce har yanzu da sauran tafiya.

https://p.dw.com/p/1DhBw
Hoto: picture-alliance/dpa

Babu dai zato ba kuma tsamanni, Abujar da ta share tsawon lokaci tana kai kawo a tsakaninta da Chadi, tace makwabciyar tata da ke gabas ta saka baki har an kai ga tsagaita wuta a tsakaninta da abokan rikicin ta na kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai, abun kuma da ya kai ga sabon fata cikin kasar da ta dauki lokaci tana jiran ganin karshen rikicin dama wajen da ke fadin tura ta kai bango kuma hakuri na shirin zuwa karshe a mataki na kasa da kasa.

Murna ta koma ciki

To sai dai kuma kasa da makwanni biyu, murna ta kai ga shiga cikin ciki ga daukaci dama wajen kasar, sakamakon furucin mahukuntan da ke fadin har yanzu fa ba sukai ga cimma tsai da wutar ba. Duk da cewar dai a fadar masu mulkin kasar ta Najeriya ana tattaunawar, har ya zuwa yanzu ba'a kai ga kaiwa ga tudun tserar da kasar da ke tsaka a cikin rudani ba.

Godswill Akpabio dai na zaman gwamnan jihar Akwa Ibom kuma daya a cikin mahalarta wani taron nazarin batun tsaron cikin gidan kasar ta Najeriya, kuma a fadarsa akwai karin gishiri dama riga mallam cikin masallaci, ga batun tsagaita wutar da a kai ta kururutawa a kasar.

Zanga-zanagr neman sako 'yan matan Chibok a Najeriya
Zanga-zangar neman sako 'yan matan Chibok a NajeriyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

“Ba wata yarjejeniyar da aka cimma har yanzu. Ina jin 'yan jarida basu fahimci labarin dai-dai ba. Har yanzu ana tattaunawar, amma abun da ya fito fili daga tattaunawarmu da mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin tsaro shine shugaban kasa zai yi duk abun da ya dace domin ganin sakin 'yan matan nan dama kare lafiya da kaddarori, wannan ya hada da sulhu inda aka samu mutanen da za'a yi sulhu dasu, saboda ba za'a yi sulhu da mutanen da basu da fuska ba.”

Kokarin saka fuska a cikin ganga ta jiki ko kuma kokari na kara shiga rudani dai sabon matsayin na zuwa ne a dai dai lokaci da yankin na arewa maso gabas dama daukacin kasar ke kara shiga hali na rashin tabbaci a halin yanzu. Akalla kananan hukumomi takwas da ke Borno dai na daukar umarni ne daga fadar Shekau yanzu haka, banda kuma Mubi da aka sauyawa Suna zuwa Madinatul Islam ga kungiyar da ke dada karfi da cin karenta har gashinsa.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da tawagarsa
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da tawagarsaHoto: picture alliance/AP Photo

Gwamnati na sheka karya

A fadar Dr Emma Shehu da ke fafutukar tabbatar da ceto 'yan mata 'yan makaranta na Chibok ke dada nuna gazawa dama halin karya a bangaren mahukunta.

“Shi Hassan Tukur da yake jagorantar wannan yarjejeniyar karyar ya dage akwai yarjejeniya, shi Danladi Ahmadu haka yace shima ministan harkokin wajen Chadi ya fada, haka Doyin Okupe da Mike Omeri daga karshe sun fito sun ce ba yarjejeniya sun kunyata kansu kuma darajar Najeriya ta fadi, shugaban kasa ba shi da niyyar ganin karshen wannan matsalar saboda in aka bi diddigi akwai abun da yake son suyi wa jihohin Arewa.”

Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin rikicin dake kara kusantar zabukan Tarayyar Najeriya dama jefa makomar kasar cikin rudani.