1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasuwar mai fafutukar 'yancin Sahrawi

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 1, 2016

Kungiyar Polisario Front da ke fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Sahrawi a kasar Moroko ta sanar da rasuwar shugabanta Mohamed Abdelaziz.

https://p.dw.com/p/1Iy3O
Jagoran fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Saharawi Mohamed Abdelaziz
Jagoran fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Saharawi Mohamed AbdelazizHoto: Getty Images/AFP/P.P.Marcou

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta nunar da cewa Abdelaziz wanda ya dade yana fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin na Sahrawi, ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. Abdelaziz dai ya jagoranci kungiyar ta Polisario Front na tsahon kusan shekaru hudu. Rasuwar tasa dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da makomar yankin na Sahrawi ke cikin rashin tabbas, bayan da mahukuntan kasar Moroko suka fatattaki mafiya yawan jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin.