1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tazarce na kara karbuwa a Rwanda

Yusuf BalaOctober 29, 2015

Shirin tazarcen da Amirka da ma sauran kasashe da ke bada tallafi ga kasar ta Rwanda suka yi watsi da shi.

https://p.dw.com/p/1GwrA
Paul Kagame
Shugaba Paul KagameHoto: Reuters/A. Kelly

'Yan majalisar wakilai a kasar Rwanda sun kada kuri'a a ranar Alhamis din nan inda suka nuna goyon bayansu na cewa shugaba Paul Kagame ya yi tazarce bayan kammala wa'adin mulki na biyu a shekarar 2017, abin da Amirka da ma sauran kasashe da ke bada tallafi ga kasar suka yi watsi da shi.

Wannan mataki dai har ila yau za a gabatar da shi a gaban majalisar dattawa har ma dai ta kai ga kuri'ar raba gardama sai dai masharhanta na ganin cikin duka wadannan matakai shirin tazarcen ba zai fiskanci wata tirjiya ba.

'Yan majalisar dai da ke zama mafi akasari masu goyon bayan shugaba Kagame sun tattauna kan wannan batu bayan gabatar da wannan bukata da masu neman yin kwaskwarimar ga kundin tsarin mulkin kasar su sama da miliyan uku suka amince da ita, ganin yadda suke kallon tsohon dan tawayen shugaban nasu ya taimaka wajen sake gina kasar da yakin basasar shekarar 1994 ya daidaita ta. Shi dai shugaba Kagame kawo yanzu bai fito ya bayyana ba ko yana so ya sake tsayawa takara.