1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Bundestag ta amince Jamus ta taimakawa Mali

January 31, 2013

Jamus ta shiga tawagar gamayyar ƙasa da ƙasa da ke ƙoƙarin ƙwato yankin arewacin Mali da kuma taimakawa ƙasar ta koma kan doka da oda .

https://p.dw.com/p/17VFa
French Foreign Affairs Minister Laurent Fabius (R) speaks with Mali president Dioncounda Traore during the international donor conference on Mali at the African Union (AU) headquarters on January 29,2013 in Addis Ababa. The donor conference opened today to drum up funds and troops to help the military operation against Islamist militants in Mali. AU Peace and Security Commissioner Ramtane Lamamra said Monday the African-led force for Mali (AFISMA) will cost $460 million, with the AU promising to contribute an 'unprecedented' $50 million for the mission and Mali's army. AFP PHOTO/SIMON MAINA (Photo credit should read SIMON MAINA/AFP/Getty Images)
Shugaban ƙasar Mali Diouconda Traoré da ministan harkokin wajen Faransa Laurent FabiusHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Jiya ne Majalisar Dokokin Bundestag ta yi muhawara game da tallafin da Jamus za ta baiwa Mali, a daidai lokacin da ƙasar ta shiga gwagwarmaya ƙwato yankinta na arewa, da masu tsatsauran kishin addinin Islama suka mamaye.

Tun lokacin da Faransa ta ƙaddamar da yaƙin belin arewancin ƙasar Mali ƙasashen Turai da dama suka baiyana aniyar bada haɗin kai ga Faransa domin cimma burin da a ka sa gaba.A nata ɓangare gwamnatin Jamus ta tsara nau'o' in tallafin da ta ke da burin kaiwa ƙasar Mali, da zaran ta samu haɗin kai daga Majalisar Dokokin Bundestag.

A muhaura da suka shirya jiya, 'yan majalisar Bundestag sun yanke shawara cewar babu gudu babu ja da baya, Jamus za ta shiga sahun ƙasashen duniya domin belin ƙasar Mali.Saidai sun yi na'am da cewar Jamus ba za ta shiga filin daga ba.

Za ta fi bada fifiko ga taimakon raya ƙasa da kuma bada horo da sojojin Mali.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) spricht am 22.01.2013 im Bundestag in Berlin bei einer gemeinsamen Sitzung des Bundestages und der französischen Nationalversammlung. Am 22.01.1963 wurde der deutsch-französische Freundschaftsvertrag in Paris unterzeichnet. Foto: Maurizio Gambarini/dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Majalisar BundestagHoto: picture alliance / dpa

A jawabin da ya gabatar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya baiyawa wajibcin kai ɗauki ga yankin arewacin Mali kuma ya bada dalilai:

Ya ce:Arewacin Mali yanki mai fama da matsaloli da dama.Saboda haka ne ma ya ke yawan fuskantar matsaloli.Banda taimakon raya kasa domin bunƙassa tattalin arzikin yanki da kyatata rayuwar al'umarsa, za mu bada gudumawa a ƙoƙarin laluben hanyoyin warware rikicin ta hanyar siyasa.

Jamus ta yi alƙawarin ware tsabar kuɗi dallar Amurika miliya 10 zuwa 120.A yayin da ta ke tsokaci game da taimakon Jamus a Mali tsofuwar ministar taimakon raya ƙasa Heidmarie Wieczorek-Zeul ta baiyana buƙatar ganin yunƙurin ƙwatar yankin arewacin ƙasar na tafiya ƙafa da da ƙafada da shirye-shiryen zaɓe ta na cewa:A daidai lokacin da hukumomin a fadar mulki ta Bamako ke ƙoƙarin maida doka da oda yankin arewa, wajibi ne su kiyaye da kare haƙƙoƙin jama'a, sannan kuma su cigaba da shirin zaɓe, wanda zai maiyar da Mali bisa tafarkin demokraɗiya.

Game da matakin da ƙungiyar Tarayya Turai ta dauzka na tura dakarun da za su bada horo ga sojojin Mali, a cikin wata mai kamawa ne ,Majalisar Dokokin Bundestag za ta muhaura domin tantance yawan sojojin da Jamus za ta aikawa a cikin wannan tawaga.

A yayin da a ɓangare daban-daban na duniya ƙasashe ke cigaba da shiyre-shiryen bada taimakon ga ƙasar Mali sojojin Faransa da na Mali na cigaba da ƙwace biranen da ke ƙarƙashin ƙungiyoyin masu tsatsauran kishin addinin Islama ɗaya bayan ɗaya.

A jimilce su na cimma wannan nasarori ba tare da fuskantar turjiya mai tsanani ba,ko da shi a wannan Alhamis sojoji biyun na ƙasar Mali sun rasa rayuka, sakamakon tarwatsewar wata bam da motarsu ta taka, tsakanin Hombori da Douenza.

Brussels, Belgium, January 17, 2013. - German Minister for foreign affairs Guido Westerwelle (L) shakes hand with the Mali Minister of Foreign Affairs & Intl. Cooperation Tieman Coulibaly (R) prior to a bilateral meeting in the EU Council headquarters. Photo: Thierry Monasse/DPA (re-cropped version) +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Guido Westerwelle da ministan harkokin wajen Mali Tieman CoulibalyHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban riƙwan ƙwaryar ƙasar Mali Pr Dioucounda Traoré a cikin wata hira da kafofin sadarwa ya ce a shirye suke su hau teburin shawara da ƙungiyar tawayen MNLA domin nazarin cimma yarjejeniya,amma shugaban yayi watsi da tayin ƙungiyar MIA wadda ta ɓalle daga Ansar Dine.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani