1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Dunia ta kaddamar da dokar yaki da cin hanci da rashawa

December 14, 2005
https://p.dw.com/p/BvGU

Yau ne dokar yaki da cin hanci da rashawa, a karkashin Majalisar Dinkin Dunia ke fara aiki.

Wannan doka da aka bullo da ita, tun shekaru da su ka wuce, na dauke da burin tallafawa kasashe dunia, su yaki annobar cin hanci da rashawa, da ke tagayyara tattalin arziki kasashe mussamman masu tassowa.

Shugaban Hukumar Majalisar Dinki Dunia, mai yaki da cin hanci da rashawa, da kuma yaduwar miyagun kwayoyi, ya sanar cewa, a ko wace shekara,a kalla kudade billiyar 840 ne ,ke tafiya, ta hanyar cin hanci da rashawa ,a dunia ta fanoni daban daban.

Shugaban yayi, suka da kakausar halshe, ga kasashen da su ka yi kaurin suna ta wannan al´amari , ya bada missalin tarayya Nigeria, inda a cewar sa ,mirganyi shugaban kasa sani Abacha, yayi rabda ciki, da dukiyar jama´a kimanin dalla Amurika, biliar 4 da rabi.

Babban matakin da sabuwar dokar ta Majalisar Dinkin dunia ta dauka, shine na kwace dukiyar duk mutumen, da a ka tabatar da, ya same ta ne, ta hanyar cin hanci da rashawa ko kuma handama.

Bugu da kari, daga yanzu, dokar ta tanadi mataki na mussaman wanda bankunan da ke ajje da irin wannan kudade,na haram,za su iya mika su, ga Majalisar Dinkin Dunia.