1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Dunia ta yi shelar tallafawa Somalia

December 14, 2005
https://p.dw.com/p/BvGP

Majalisar Dinkin Dunia, ta tara kokon bara, da burin tattara a kalla, dalla million 174 domin bada taimakon raya kasa ,ga Somalia, da ke fama da yake yake, tun shekara ta 1991.

Wakilin Majalisar DinkinDunia mai kulla da Somalia, a wani taron manema labarai, da ya shirya ya bayana cewa a halin da a ke ciki fiye da mutane dubu dari 3 ,ke fama da matsananciyar yinwa a wannan kasa, a yayin da mutane dubu dari 4 su ka shiga uwa dunia, don tsira da rayukan su, a sakamakon hare hare da yake yaken bassasa, da ke ci gaba da wakana.

Munate da su ka rugumi kaddara, su ka tsaya a gidajen su, na fama da cuttutuka daban daban da rashin aikin yi, da taka hakoki, ta fannoni da dama.

A shekara da ta gabata an girka sabin hukumomi a kasar, to amma ,su na fama da rabuwar kanu, abinda ke jawo cikas, ga ci gaban da ake bukatar samu.

Yakin Somalia, ya hadasa mutuwar mutane dubu dari 3 zuwa dubu 5, inji alkalumman Majalisar Dinkin Dunia.