1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a kama masu fasakaurin mutane ta cikin teku

Yusuf BalaSeptember 19, 2014

Dubban mutane dai ke rasa rayukansu a lokacin da suke neman barin kasashensu zuwa Turai ta barauniyar hanya da suka hadar da bin jiragen ruwa da a lokuta da dama suke nitsewa a teku.

https://p.dw.com/p/1DFy9
UNHCR-Logo
Hoto: UNHCR

Manyan jami'ai daga Majalisar Dinkin Duniya sun nemi kasashen arewacin Afirka da nahiyar Turai, su tabbatar da ganin an gurfanar da mutanen da suka yi jigilar 'yan gudun hijira kimanin 500 da suka rasu a tekun Bahar Rum bayan da jirginsu ya nitse a kan hanyarsu a makon da ya gabata.

Zeid Ra'ad Al Hussein kwamishinan kare hakkin bil Adama a ofishin na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa idan har wannan adadi ya tabbata, zai kasance babban kisan gilla mai girma a tekun na Bahar Rum.

Zeid wanda tsohon jami'in diflomasiya ne kuma dan sarauta daga gidan sarautar Jordan ya ce wadannan kasashe su tashi tsaye su tabbatar da ganin an kama wadannan mutane da ke aikin fasakaurin 'yan gudun hijira, da suka sanya rayuwar wadannan mutane cikin hadarin da ya yi sanadin rayukansu don kawai wata riba da suke neman samu.

Ya zuwa yanzu dai mutane 11 ne kawai aka samu da rai bayan da jirgin da ya dauko su ya kife bayan ya bar kasar Masar.