1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Faransa ta amince da Falasɗinu

Abdourahamane HassaneDecember 2, 2014

'Yan majalisar dokokin sun amince da wani daftarin ƙudirin da gaggarumin rinjaye wanda ya yi kira ga gwamatin Faransa da ta amince da Falasɗinu a matsayin yantacciyar ƙasa.

https://p.dw.com/p/1DyOE
Frankreich Nationalversammlung Sitzung Debatte
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙudirin wanda ba na dole ba ne, wanda masu rinjaye na jam'iyyar 'yan gurguzu da ke yin mulki suka gabatar ya sha suka daga jam'iyyar 'yan mazan jiya.

Hukumar Falasdinawa ta OLP ta yi marhabinn da ƙudrin sannan kuma ta yi kira ga gwamnatin Faransa da ta bi sahu. Tuni da Isra'ila ta bayyana takaicinta a kan wannan yunƙuri, kuma kawo yanzu ƙasashe 135 suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken yanci.