1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Iraki ta fara zama

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv14
A yau asabar majalisar dokokin Iraqi ta yi zama bayan da kawancen jam´iyun ´yan shi´a dake mulki a kasar ya nada Jawad al-Maliki a matsayin sabon dan takararta a mukamin FM. Wannan ci-gaban da aka samu bayan an shafe watanni 4 ana fama da dambaruwar siyasa, ya bawa majalisar dokokin damar kaddamar da shirin kafa sabuwar gwamnati da nufin ceto kasar daga fadawa wani rikicin kabilanci. Adnan Pachachi kakakin majalisar na riko ya bude zaman majalisar a yankin nan na tsaro da aka fi sani da Green Zone. Kafin fara zaman dan majalisar na bangaren shi´a Ridha Jawad Taqi ya ce dukkan bangarorin sun amince da wani shirin raba manyan mukamai wanda ake sa rai majalisar zata kada kuri´a a wani lokaci yau din nan. Jalal Talabani na bangaren kurdawa zai saura akan mukamin shugaban kasa a wani wa´adi na biyu yayin da dan Sunni Tariq al-Hashimi da kuma dan shi´a Adil Abdul-Mahdi zasu rike mukamin mataimakan shugaban kasa.