1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Krimeya ta kada kuri'ar hadewa da Rasha

March 6, 2014

Wakilan majalisar sun kuma tsayar da 16 ga wata Maris a matsayin ranar kada kuri'ar raba gardama game da makomar yankin na Krimeya mai ikon cin gashin kai.

https://p.dw.com/p/1BLDj
Hoto: Reuters

Kamfanin dillancin labaran Rasha wato RAI, ya rawaito cewa majalisar dokokin yankin tsibirin Krimeya na kasar Yukren ta amince da hadewar wannan jamhuriya mai cin gashin kai da kasar Rasha. Wakilai 78 daga cikin 81 da ke majalisar sun kada kuri'ar amincewa da shiga cikin Rasha, sannan a lokaci guda 'ya'yan majalisar sun dawo da kuri'ar raba gardama game da makomar Krimeya, makonni biyu gaba da wa'adi, zuwa ranar 16 ga watannan na Maris. Kuri'ar dai za ta ba wa al'umma damar zabi ko jamhuriyar mai 'yancin cin gashin kanta ta ci gaba da zama cikin kasar Yukren ko kuma ta hade da Rasha. Sabbin mahukuntan birnin Kiev sun bayyana wannan kuri'ar raba gardamar da ake shirin yi a Krimeya da cewa haramun ne. Tun bayan hambarar da shugaban Yukren Viktor Yanukovych, masu goyon bayan Rasha a yankin tsibiri suka karbi ragamar mulki. Rahotanni daga Mosko sun ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya fara nazari a kan matakin majalisar ta Krimeya kuma yana tattauna batun da majalisar tsaron kasa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Usman Shehu Usman