1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Turai ta cimma yarjejeniya a game da kasafin kudi

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv32

Majalisar tarayyar turai tare da kasashen kungiyar EU sun cimma yarjejeniya a game da kasafin kudin kungiyar na 2007 zuwa 2013. Majalisar ta amince da ƙari a kan kasafin da shugabanin kungiyar tarayyar turan suka cimma a watan Disambar bara, daga euro biliyan 862.4 zuwa euro biliyan 864.4, tun da farko majalisar ta buƙaci ƙarin euro biliyan 12 domin kyautata hanyoyin sufuri da fannin nazarin bincike da kuma bunkasa shaánin ilimi. To amma gwamnatocin tarayyar turan sun bukaci yin taka tsantsan wajen kashe kuɗaɗe musamman a daidai wannan lokaci da ƙasashen ke ƙoƙarin rage gibi na kasafin kuɗi. Ministan kudi na ƙasar Austria Karl Heinz Grasser, ya baiyana gamsuwa da cimma yarjejeniya a game da kasafin kuɗin wanda kasashen turan suka dade suna tafka muhawara a kan sa. Babban abin armashi a game da kasafin shi ne amincewa da ƙudirin sassauci na baiwa hukumomi tsara yadda zaá kasafta kashe kuɗaɗen da suka yi rara, da kuma baiwa majalisar tarayyar turan ƙarin iko na yin nazarin kasafin kuɗin a shekarar 2008 zuwa 2009. Fiye da kashi 40 cikin dari na kasafin kuɗin zai tafi ne ga ɓangaren noma, kashi ɗaya bisa uku ga gudunmawar jin ƙai da raya ƙasa, kana ragowar kason zaá kashe su ne ga harkar mulki da tsaro da kuma taimakawa ƙasashen ketare.