1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilai ta kira sifeto janar na 'yan sanda

Uwais Abubakar IdrissNovember 21, 2014

Kwamitin kula da harkokin 'yan sanda na majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa ba zai lamunci duk wani mamaye daga ‘yan sandan Najeriyar a majalisar ba abin da suka ce ya sabawa tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/1DrNF
Hoto: DW/U. Musa

Kutsen da 'yan sandan Najeriya suka yi har da kai su ga afka wa cikin zauren majalisar tare da fesa hayaki mai sa kwalla a kan 'yan majalisa da dama ne ya sanya kwamitin gayyatar Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya Sulaiman Abba domin ya yi masu bayyanin yadda aka yi wannan lamari ya faru wanda ke ci gaba da fuskantar nuna damuwa a kan illar da hakan zai yi ga demokaradiyya Najeriyar. Sifeto Janar din, ya tura Mataimakinsa mai kula da harkokin gudanarwa ya wakilce shi watau Sotonye Wakama don ya yi masu bayani, abun da ya fusata 'yan majalisar da dama bisa cewa nauyi da ma illar matsalar ta wucce a ce an turo wani wakili don ya yi masu bayani. Hon Rufa'I Ahmed Chanchangi bayyana dalilansu da kin amsar wakilcin nashi.

Symbolbild Nigeria Polizei
Hoto: imago/Xinhua

"Kasar nan dai tafi kowa daga cikinmu tafi ni tafi shugaban kasa, in ba kasar, ba za'a yi shugaban kasa ba, ba za'a yi shugaban ‘yan sanda ba, don haka dole mu kare mutuncin kasar nan a duk inda muke, kuma abin da ya nada shi kundin tsarin mulkin kasa ne, kuma abin da muke aiki da shi kundin tsarin mulki ne, saboda haka ba zamu saurari wakilinsa har sai ya zo ya gabatar da kan shi a gaban majalisa. Don akwai matakan da muka shiryawa irin wadanda ke kin zuwa majalisa , kuma in Allah ya yardda za mu yi amfani da wannan matakin mu gabatar das hi a gaban majalisa"

Dukkanin kokarin da muka yi don jin ta bakin Mataimakin Sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar DIG Sotonye Wakama ta ci tura domin ko da a zaman da aka yi yaki cewa uffan bisa matakin da 'yan majalisar suka dauka. Ahmed Baba Kaita na majalisar wakilan Najeriya ya bayyana tsoron inda aka dosa a dambarwarar siyasar da ta sa Najeriyar a gaba ana sauran 'yan makwani a gudanar da zabe, a lokacin da yakamata a samu Karin daidaito ga dimmukurdiyyar.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

"Ai kaga irin wadannan abubuwa da ke sa a banzantar da demokaradiyya kanta saboda ai abin da ya faru ba shugaban majalisa Aminu Tambuwar aka yi wa ba, kuma ba jam'iyyar adawa ta APC aka yi wa ba wannan majalisar wakilai aka yi wa ta Najeriya. Kuma dimukurdiyya ake taimakawa yaushe zamu tashi mu ce a daina irin wannan, shin in ba'a dauki dokar yadda take ba ina za mu je ne?'"
Abin jira a gani shi ne ko sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar zai bayyana a gaban majalisar datawa a ranar Talata domin ammsa irin wannan ba'asin, tare ma da sa ido don ganin makomar dokar ta bacin da 'yan majalisar za su sake zama domin yiwuwar mahawara a kanta.