1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilai ta Najeriya ta amince da dokar ta-ɓaci

Umaru AliyuMay 15, 2014

Majalisar ta amince da dokar ta-ɓacin ne a daidai lokacin da wasu sojoji a Barno suka yi bore, kana kuma su iyayen 'yan mata Chibok suka yi tsokaci a kan matakin gwamnatin na ƙin tattaunawa da Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1C0hH
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Boren da wasu sojojin Najeriya suka yi a Maiduguri ya janyo da buɗe wuta ga motar da ake ɗauke da shugaban rundunar Sojojin da ke garin, ya haifar da zazzafan martani daga masana tsaro da sauran ‘yan Najeriya wanda suke ganin gaskiyya ce ta fara bayyana.

Sojojin Borno sun ce ba za su yaƙi Boko Haram ba sai a biya musu buƙatunsu.

Rahotanni daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na nuna cewar wasu sojoji da suka fusata sun harbi motar shugaban rundunar sojoji na birnin, Manjo Janar Ahmed Mohammed. Sojojin dai sun fusata ne sakamakon abin da suka kira rashin kulawa da buƙatunsu daga shugabanninsu inda kuma suka zargi Shugabannin da yi musu turin jeka ka mutu a yaƙin da suke yi da Ƙungiyar Boko Haram.

Nigeria Bodentruppen
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Al'ummar arewacin Najeriya na yin adawa da matakin gwamnatin na ƙin tattaunwa da Boko Haram

A wani labarin kuma iyayen daliban da Ƙungiyar Boko Haram ke garkuwa da su sun ƙara faɗawa cikin tashin hankali bayan da gwamnatin Najeriya ta shure tayin da Ƙungiyar Boko Haram ta yi na yin musayar membobinta da ake tsare da su da ‘yan matan nan da ta kame a garin Chibok. Iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki da sauran ‘yan Najeriya wanda suka bayyana farin cikin ganin ‘yan matan a raye sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta sake tunani kan matsayinta.

Demonstration Boko Haram Nigeria 14.05.2014
Hoto: Reuters

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Abuja Ubale Musa ya aiko mana a kan zaman taron majalisar dokokin da kuma hira da Mouhamadou Awal Balarabe ya yi da Tukur Abdulƙadir masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Kaduna t

Mawallafi: Muhammad Al-Amin
Edita : Abdourahamane Hassane