1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Ayyukan Deutsche Welle

May 4, 2004

Kwararrun masana al'amuran yada labaru da jami'an siyasa da 'yan kasuwa suna gudanar da taron bita akan sabuwar alkiblar da Deutsche Welle zata fuskanta a ayyukanta na yau da kullum

https://p.dw.com/p/Bvk2
Mahalarta taron tattaunawa akan makomar ayyukan DW
Mahalarta taron tattaunawa akan makomar ayyukan DW

Bana ake sa ran cewar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag zata albarkaci wata sabuwar doka a game da makomar ayyukan tashar Deutsche Welle. A shawarar da gwamnati ta zayyana an ba da la’akari sosai da sosai a game da yadda duniya ke dada kasancewa tamkar rumfa daya. A sabili da haka nan gaba ba matsayin Jamus kadai ne za a rika ba da la’akari da su a shirye-shiryen da Deutsche Welle take gabatarwa ba, kazalika har da na sauran sassa a game da siyasar duniya. To sai dai kuma a hakikanin gaskiya tuntuni tashar ke fuskantar wannan alkibla a shirye-shiryenta na yau da kullum. Babban misali a nan shi ne shirin tashar na Mu Kewaya Turai, wanda ya sha hara tsakanin masu sauraro ba ma kawai a nahiyar Turai kadai ba har da sauran sassa na duniya. Wannan shirin, kamar yadda shugaban Deutsche Welle Etik Bettermann ya nunar, ya taimaka wajen bayyanarwa da jama’a irin matsayin da Jamus ke dauke da shi a hada-hadar hadin kan nahiyar. Bettermann sai ya kara da cewar:

Ba shakka Deutsche Welle zata ci gaba da kasancewa tashar Jamus dake yada shirye-shiryenta zuwa kasashen ketare. Amma wani abin da ya kamata a ba da la’akari da shi shi ne gaskiyar cewa kasar Jamus ta samu tasirin yankunan gabaci da yammaci da arwaci da kuma kudanci a cikin tarihinta, kuma a sakamakon haka nike tattare da ra’ayin cewar muna da cikakkiyar kafa ta ba da gudummawa gwargwadon iko domin kyautata dangantakun kasa da kasa da tabbatar da ‚yancin ‚yan jarida a duniya baki daya.

To sai dai kuma makomar ayyukan tashar ta Deutsche Welle ta ta’allaka ne akan yawan kudin da ake kasafta mata. Domin kuwa an yi shekara da shekaru tashar na fama da radadin matakan tsumulmular kudi da gwamnati ke dauka. An kayyade yawan kasafin kudin tashar daga Euro miliyan 320 a shekarar 1999 zuwa Euro miliyan 280 a halin yanzu haka. Bugu da kari kuma akwai wasu matakan tsumulmular kudin da zasu biyo baya duk kuwa da karin nauyin da aka dora mata, misali shirye-shiryen telebijin da take yadawa zuwa kasar Afghanistan wanda tuni aka fara shawarar dakatar da shi, kazalika da shirinta na harshen Sanisanci dangane da kasashen Latin Amurka duk kuwa da muhimmancin da dukkan shirye-shiryen guda biyu ke da shi ga wadannan yankuna. A bangare guda dai ana neman ganin Deutsche Welle ta taka wata muhimmiyar rawa wajen yada nagartattun labarai zuwa yankunan da ake take hakkin ‚yan jarida, sannan a daya bangaren kuma ana fatan ganin ta zama wata gada ta sadarwa da wayar da kan masu sauraro a kasashen ketare a game da manufofin Jamus da harshen al’umar kasar da kuma al’adunsu kamar yadda aka ji daga bakin ministar al’adu da kafofin yada labarai ta Jamus Christina Weiss.