1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar dakarun Faransa a Mali

November 5, 2013

Faransa ta ce ba za ta jinkirta wa’adin da ta ɗeba na janye dakarunta daga Mali ba, duk da harin da yayi sanadiyyar ‘yan jaridar kasarta

https://p.dw.com/p/1ABnJ
FILE- in this Oct. 11, 2012 file picture, France's Foreign Minister Laurent Fabius speaks at a press conference at French Foreign Ministry in Paris. Fabius told Europe-1 radio Sunday, Oct. 21, 2012, it's likely that Syrian President Bashar Assad's government had a hand in the assassination of Lebanon's intelligence chief Brig. Gen. Wissam Al-Hassan in a Beirut bombing. Fabius told that while it wasn't fully clear who was behind the attack that killed al-Hassan and seven others, it was "probable" that Syria played a role in the blast. (Foto:Francois Mori, File/AP/dapd)
Laurent Fabius Ministan harkokin wajen FaransaHoto: AP

Faransa ta ce ba zata jinkirta janye dakarunta daga Mali ba duk da harin da ya kai ga hallakar wasu 'yan jaridar Faransar biyu bisa bayanan da ministan harkokin wajen ƙasar Laurent Fabius ya bayar wannan talatar.

Fabius ya kuma bada tabbacin cewa Faransar ta tura dakaru 150 daga Kidal zuwa Arewacin Mali domin su taimaka wajen daidaita lamuran tsaro, ya kuma ƙara da cewa bacin matakin da shugaba Francois Hollande ya ɗauka na ƙarfafa matakan tsaro a Kidal, ba zasu sauya wa'adin da suka riga suka ɗeba na janye dakarun ba.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya rawaito cewa a 'yan kwanaki masu zuwa, za a ƙara dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar

Tun ranar litini mahukuntan Faransa suka ce suna ƙaddamar da binciken gano waɗanda ke da alhakin kisan 'yan jaridan nan Faransawa, kuma sun ce duk da cewa akwai matsalolin tsaro a arewacin ƙasar, Shugaba Ibrahim Keita ne ke da alhakin yanke irin shawarwarin da ƙasar ke buƙata, amma kuma gwamnati a Paris za ta cigaba da marawa shugaban baya wajen yanke waɗannan shawarwari.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe