1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar jam'iyyar PDP bayan murabus din Mu'azu

Ubale Musa/ASMay 20, 2015

Jam'iyyar PDP da ke shirin barin gado a Najeriya ta sanar da murabus din shugabanta Ahmadu Adamu Mu'azu daga shugabancin jam'iyyar lamarin da ke sanya ayar tambaya kan makomar jam'iyyar.

https://p.dw.com/p/1FTHr
Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Hoto: DW/U.Musa

A wata hira da ya yi da wakilinmun na Abuja Ubale Musa, mukaddashin kakakin jam'iyyar PDP din Barisster Abdullahi Jalo ya tabbatar da murabus din na Mu'azu daga shugabancin jam'iyyar ta PDP wadda ke dab da barin gado na mulki bayan da ta sha kaye a zaben shugaban kasa da na gwamnoni da aka yi a makonnin da suka gabata.

Murabus din na Mu'azu dai ya kawo karshen rade-radin da aka shafe tsawon lokaci ana yi na batu barinsa shugabancin jam'iyyar ta PDP wanda da dama ke ganin wasu jiga-jigan gwamnatin kasar da ma masu fada a ji a jam'iyyar ne ke son ganin ya sauka saboda zargin da suke masa da hannu wajen gaza tabuka abin kirki a zaben.

Tuni masana harkokin siyasa suka fara tofa albarkacin bakunansu kan wannan batu wanda wasu ke ganin zai iya raba kan jam'iyyar a wannan hali da ke ciki n arahsin gwamnati kana masanan na ganin rashin samun hadin kan 'yan jam'iyyar zai lalata lamura musamman ma na yin siyasa ta adawa kasancewar PDP din ce za ta kasance babbar jam'iyyar adawa bayan jam'iyyar APC ta haye gadon mulki a karshen wannan watan.

Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014
Na hannun daman shugaba Jonathan da wasu mukarraban PDP na ganin Mu'azu ne ummul aba'isin faduwa zaben da suka yi.Hoto: picture-alliance/AP

Ya zuwa yanzu dai babu wanda jam'iyyar ta bayyana a matsayin wanda zai jagorance ta a matsayi na riko kwarya sai dai ana hasashen kila sabon shugaban da za ta samu zai iya fitowa daga kudancin kasar inda nan ne ta fi samun tagomashi batun da ya ake kallon za ta iya komawa jam'iyya ta wani bangaren kasar maimakon jam'iyya ta kasa baki daya.