1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar tattalin arzikin Najeriya bayan Lamido

February 20, 2014

Masana tattalin arziki da 'yan siyasa na ci gaba da bayyana rashin dacewar dakatarwar da shugaba Jonathan ya yi wa shugaban Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido.

https://p.dw.com/p/1BCwx
Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria
Hoto: Reuters

A wani abun dake zaman kaiwa tik a cikin rikicin gwamnan babban bankin Tarrayar Najeriya na CBN da ya sha dauki ba dadi da kamfanin mai bisa zargin halin bera, da safiyar yau shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya tabbatar da dakatar da Sunusin tare da tura sunan sabon mutumin da yake fatan zai gajeshi gaban majalisar datawan kasar.

Ya dai kira ruwa daga dukkan alamu kuma yana shirin shan kashi, ga Gwamnan babban bankin Najeriya Sunusi Lamido Sunusi da fadar gwamnatin kasar ta ce ta dakatar daga kan mukaminsa na jami'in kudi mafi tasiri a kasar.

Da safiyar wannan alhamis din ce dai wata sanarwar fadar gwamnatin kasar ta ce shugaba Jonathan din ya kai ga yanke hukunci na dakatar da gwamnan ne bisa tabargaza dama karantsaye ga kaidojin kudi na cikin bankin, abun kuma da a fadar fadar ya sanya dakatar da Sunusin zama wajibi da nufin tabbatar da sake dora bankin bisa kyakkawan tsari.

To sai dai kuma a kusan fili take an dauki tsawon lokaci ana kai ruwa cikin rana tsakanin gwamnan da ya zargi kamfanin kudin kasar na NNPC da sama da fadi tsabar kudin da suka kai dalar amurka miliyan dubu 20 ko kuma kashi 75 cikin dari na dsaukacin kasafin kudin kasar na bana.

Abun kuma da yanzu haka ke tada jijiyar wuya cikin kasar dake kallon wakaci ka tashin da babu kamarta a matsayin tabbacin mahukuntan kasar na daurin gindi ga halin berar da ya kai kololuwa kuma ke barazana ga makomar kasar..

Zentralbank von Nigeria
Babban Bankin Najeriya

To sai dai kuma ko bayan nan dai dakatarwar dake zaman irinta ta farko a cikin tarihin bankin na shekaru sama da 50 dai na iya shafar tattalin arzikin kasar da ma tsari na kudi ga Sunusin da ya share shekara da shekaru yana lashe lambar zakaran farko a tsakanin gwamnonin bankunan kasashen nahiyar ta Africa.

Sunusin ne dai ya kai ga tabbatar da tsaftace harkokin bankunan kasar tare da dora su bisa turbar samun karbuwa dama takara da 'yan uwansu cikin dama wajen nahiyar sannan kuma ana masa kallon kashin bayan manufofin kudin kasar a idanun manyan kasashen duniya dsake fatan sake mikewar tattalin arzikin kasar da nufin zuba jari.

Abun kuma da afadar Dr Nazifi Darma dake zaman wani masanin harkokin tattalin arzikin kasar ke iya shafar daukacin harkokin kudin dama dangantakar dake tsakanin Najeriyar da masu jarin na waje.

“Wannan zai nuna cewar babu tsari na tafi da tattalin arziki dake tafiya a dunkule da kuma ke nuna shugabannin na tafiya a matsayin 'yan juna to kaga idan wannan ya samu kudaden da najeriya ke samu zai ragu kuma masu so su shigo da kudin su zasu iya fasawa”.

Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

A siyasance dai Sunusin ya jima yana zaman dan lele ga masu adawar kasar dake masa kallon jagora ga kokari na bankado cin hanci dama rashawar da tai katutu a cikin gwamnatin kasar kuma ke barazana ga demokaradiya da cigaban al'ummarta.

Abun kuma da ya kai ga jagorar adawar kasar ta APC ta sha fitowa tana bada kariya ga sunusin duk da cewar dai bai baiyyana goyon bayansa ga harka ta siyasa kuma ya dauki lokaci yan kokari na ware kansa daga hayaniyar siyasar kasar ta Najeriya.

Sallamar dai a fadar Buba Galadima dake zaman jigo a cikin jam'iyyar APC dai na dada tabbatar baki biyu a bangaren mahukuntan na Abuja dake ikirarin yaki da batun hanci amma kuma ke daurin gindi ga masu sana'ar;

“An sha zargin mutane da yawa da sama da fadi da dukar jama'a kamar Orunma Oteh ta Sec da majalisar tarrayar Najeriya da kanta tace sai an kore ta. Aka ki ce mata komai An kuma yi akan ita wannan ministan man dake a tsakiyar wannan rigima na batan kudin mai . Wai abun tambaya shine shugaban kasa bashi da iko ko hurumi na kora ko dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, majalisa ce kawai ke iya da wannan hurumi in ta bincikensa aka same shi da laifi to za'a iya korarsa”.

Tuni dai fadar ta aiyyana sunan Serah Alade a matsayin mutuniyar da zata rike aiyyukan bankin har ya zuwa tabbatar da amincewa da Mr Godwin Emefiele dake zaman shugaban bankin Zenith bank a kasar da kuma ya fito daga jihar Delta da fadar ta mikawa majalisar dattawan kasar a matsayin sabon magajin na Sunusi sannan kuma da Adelebu Adekola da zai taimaka masa kan sabon matsayinta.

To sai dai kuma akwai yiwuwar sabuwar takaddam bisa ikon dakatar da gwamnan da dokar bankin ta dora shi a hannun majlisar dattawa, da kuma tun da farko yai uwar watsi da umurnin shugaban kasar na ajiye mukamin domin kansa.

A watan Yuni mai zuwa ne dai aka tsara wa'adin gwamnan na shekaru biyar zai zo karshe, wa'adin kuma da ake yiwa kallon mai cike da sama da kasa cikin masana'antar kudin kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar