1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar tsohon shugaban Masar

July 12, 2013

Jamus ta bukaci hanzarta sakin shugaban Masar Mursi, a matsayin wani bangare na warware rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1977Y
Supporters of the ousted President Mohamed Mursi shout during a protest in Cairo July 12, 2013. Supporters of Mursi called for protests on Friday and Egyptians prayed there would be no repeat of clashes that have killed more than 90 people in the last week in the bitterly divided Arab nation. REUTERS/Suhaib Salem (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban Masar Mohammed Mursi.  A cikin jawabin da yayi a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus, mai magana da yawon ministan, Martin Shaefer ya ce  babu abin da duk wani tashin hankalin  siyasar zai haifar akan kasar ta Masar in banda jefa ta a cikin mawuyaciyar makoma.  A don haka yace, Jamus  ta bukaci da a kawo karshen tsare Mohammed Mursi da ake yi . Ya kara da cewa, akwai bukatar  ba wata kungiya ta kasa da kasa mai zaman kanta kamar ta Red Cross damar ganawa da Mursi ba da wani sharadi ba.  Ba'ada bayan haka, ana jinkirta kafa gwamnatin wucin gadi.

To sai dai firaiministan rikon kwaryar Masar, Hassam al-Beblawai  ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewar, za a kafa gwamnati  kafin karshen  mako mai zuwa. Da farko Beblawi  ya kyautata fatan kafa gwamnati a ranar Litinin mai zuwa. 

A daura da hakan  Kungiyar 'yan uwa Musulmi  da ke nuna goyon baya ga Mursi  ta ce za ta ci gaba da gudanar da zanga-zanga har sai an sake dora Mursi kan karagar mulkin kasar.

Mawallafiya : Halima Balaraba Abbas

Edita         : Saleh Umar Saleh