1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali a kan turbar demokradiyya

September 19, 2013

Yanzu dai lamura sun fara daidaita a kasar ta Mali, inda a ranar Alhamis aka yi bikin kaddamar da sabon shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita a birnin Bamako.

https://p.dw.com/p/19kak
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Kasar Mali ta kasance abin koyi ta fannin siyasa da tattalin arziki ga sauran kasashen yammacin Afirka. Amma tun bayan dagulewar harkokin siyasar kasar cikin shekara ta 2012, kasar ta tsunduma cikin rikicin Abzinawa 'yan tawaye, da ya kai ga kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula a cikin watan Maris na shekarar 2012. Yanzu lamura sun fara daidaita, inda a ranar Alhamis aka yi bikin kaddamar da sabon shugaban kasa. Shin ina ake ganin kasar ta dosa?

Manyan baki a birnin Bamako

A wannan Alhamis a birnin Bamako aka yi bikin rantsar da sabon Shugaban kasar ta Mali, Ibrahim Boubacar Keita, wanda aka rantsar tun ranar 4 ga wannan wata na Satumba. Shugaban kasar Faransa Francois Holland da sauran shugabannin Afirka da suka hada da Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire da Sarkin Maroko Mohammed VI na cikin manyan bakin da ke halartar bikin.

Members of the Malian and the Tuareg delegations shake their hands after signing an agreement at a meeting on the Malian crisis on June 18, 2013 in Ouagadougou. The Malian government and Tuareg rebels occupying a key northern city signed an accord today paving the way for presidential elections in the west African state next month. Mali's territorial administration minister and representatives of two Tuareg movements signed the deal in Ouagadougou, capital of neighbouring Burkina Faso, as the lead mediator in negotiations, Burkinabe President Blaise Compaore, looked on. AFP PHOTO AHMED OUOBA (Photo credit should read AHMED OUOBA/AFP/Getty Images)
A cikin watan Yuni gwamnatin Bamako ta kulla yarjejeniyar wucin gadi da wakilan AbzinawaHoto: AHMED OUOBA/AFP/Getty Images

Daya daga cikin muhimman batutuwa da sabon shugaban Mali Boubakar Keita zai saka a gaba sun hada da rikicin arewacin kasar, na 'yan tawayen Abzinawa da ya janyo sojoji suka kifar da gwamnatin cikin watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2012.

Henner Papendieck na Gidauniyar GIZ ta Jamus, masani ne, wanda ya shafe shekaru yana aiki bisa shirin tallafa wa manoma da inganta harkokin kasuwanci. Inda ya ce ba daukacin al'ummar kasar 'yan tawayen ke magana da yawunsu ba:

***Achtung: NUR zur Berichterstattung über das Programm MALI NORD verwenden!*** Fotografin Barbara Papendieck, Rechte frei fuer Berichterstattung ueber Programm Mali Nord *** undatiert, eingestellt im März 2012
Henner Papendieck ya kwashe shekaru masu yawa yana aikin taimakon raya kasa a arewacin MaliHoto: DW/K. Gänsler

"Ba sa wakiltar daukacin al'ummar kasar. Abin da ya dace shi ne dawo da 'yan gudun hijira domin sanin matsayinsu kan makomar kasar."

'Yan tawaye na da nasu shakkun

'Yan tawayen arewacin kasar ta Mali na kungiyar MNLA, wadanda suka kwashe shekaru suna gwagwarmayar neman kafa kasar Azawad, sun fahimci cewa amfani da karfi ba zai taba zama mafita ba. Kakakin kungiyar a kasashen Turai Moussa Ag Assarid ya bayyana babban burinsu na gaba yana mai cewa:

"Ba ma adawa da matakin saka kungiyoyin fararen hula cikin shirin tattaunawa. Abin da ba ma bukatar ya sake faruwa shi ne, tattara duk karfi ga gwamnatin tsakiya kamar yadda ya faru a shekarar 1992."

:DW_Mali_Flüchtlinge4: Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 15. Mai 2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Déou, Burkina Faso
Da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar arewacin Mali sun samu mafaka a kasashe makwabtaHoto: Barbara Papendieck

Dubban 'yan gudun hijirar kasar ta Mali da ke kasashen ketare, suna cikin masu tofa albarkacin bakinsu kan makomar kasar. Nina Wallet Intalou tana cikin wadanda suka tsere zuwa kasar Mauritaniya, ta yi nuni da cewa:

"Mahukuntan birnin Bamako ba sa mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta. Ba su saki fursunoni ba, kuma suna kame manoma da sauran al'umma babu kakkautawa."

Dakarun Faransa sun taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin kasar ta Mali. Kuma bayan bikin kaddamar da sabon Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ake wa lakabi da IBK, a wannan Alhamis, sabon shugaban yana da jan aikin mayar da martabar kasar tsakanin sauran kasashen duniya, da dinke barakar da aka samu tsakanin 'yan kasa.

Mawallafa: Dirke Köpp / Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani