1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta ce ba za tattauna da Ansar Dine ba

January 31, 2013

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Dioncounda Traore ya ce gwamnatinsa shirye ta ke da ta tattauna da 'yan kungiyar MNLA amma ya ce ba zai tattauna da 'yan Asar Dine ba.

https://p.dw.com/p/17Uw0
Dioncounda Traore, Mali's parliamentary head who was forced into exile after last month's coup, is seen after arriving at the airport to take up his constitutionally-mandated post as interim president, in Bamako, Mali Saturday, April 7, 2012. Traore's return comes after coup leader Capt. Amadou Haya Sanogo signed an accord late Friday, agreeing to return the nation to constitutional rule.(Foto:Harouna Traore/AP/dapd)
Dioncounda Traore Mali PräsidentHoto: AP

Shugaba Traore ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan radiyo Faransa na RFI, inda ya ce duba da halin da ake ciki a kasar, ta tabbata cewar kungiyar Ansar Dine ta rasa dukannin damar da ta ke da ita ta sasantawa da gwamnati.

Dangane da kunguyar Azawad kuwa wadda a makon jiya ta ce ta yi watasi da kawancen ta da Ansar Dine, shugaban na Mali ya ce wannan labarin ba abin dauka ba ne duk kuwa da cewar kungiyar ta nesanta kanta daga duk wata alaka da kungiyar Al-Qaida ta yankin Magreb.

Da ya juya kan yakin da Faransa ke jagoranta a kasar kuwa da nufin fatattakar 'yan tawaye, Mr. Traore ya ce sojinsu da na kasashen waje za su yi bakin kokarinsu wajen kakkabe 'yan tawayen daga kasar nan da dan kankanin lokaci.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu