1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta cimma yarjejeniya tsakanita da 'yan tawaye

Walton, LuciaFebruary 20, 2015

Gwamnatin ƙasar Mali ta cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da wasu ƙungiyoyin mayaƙan sa kai da ke a arewacin ƙasar

https://p.dw.com/p/1EetZ
Algerien Mali Waffenruhe in Algier vereinbart Bilal Ag Acherif und Ramtane Lamamra
Bilal Ag Acherif na MNLA da Ramtane Lamamra ministan harkokin waje na Aljeriya.Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

An dai cimma wannan yarjejeniya a jiya Alhamis a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Algers na Aljeriya.

Ƙungiyoyin da suka saka hannu a kan yarjejeniyar su ne Ƙungiyar 'yan tawaye ta abizinawa ta AZAWAD wato MNLA da Ƙungiyar CM-FPR da kuma wasu ƙungiyoyin guda biyar.Ministan harkokin waje na Aljeriya Ramtane Lamara ya ce dukkanin ɓangrorin sun amince su dakatar da fadan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman