1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Taron Afirka da Faransa karo na 27

Abdourahamane Hassane
January 13, 2017

Kungiyoyin matasa na nahiyar Afrika da kuma Faransa sun gudanar da taron share fage gabannin babban taron kuma batun da suka tattauna shi ne na shigar da matasa a cikin harkokin jagoranci na kamfanoni.

https://p.dw.com/p/2Vly7
Hollande und Keita in Paris 01.10.2013 Abreise
Shugaban Faransa Fransoi Hollande da na kasar Mali Ibrahim Boubacar KeitaHoto: Reuters

Matasan na Afirka da Faransa sun tattauna wannan batu ne saboda irin mahimmanci da yake da shi ga tattalin nahiyar ganin cewa yawan al'ummar ta Afirka galibinta matasa ne masu tasowa. A kowace shekara a nahiyar ta Afrika da ma Faransa ana bukatar sabbin gurabban aiyyuka kamar mutum miliyan goma, saboda haka akwai buklatar yan siyasar sun saka hannu a cikin lamarin domin ci gaba a kasahen. Fatuma Sangho shugabar wata kungiya mai fafutukar neman ci-gaban Afrika da ta hallarci taron ta yi tsokaci a kai:

DW Africa on the move Mali
Amadou Thiam wani matashin dan siyasa a MaliHoto: DW/M. Meier

"Muna sa rai ba ya ga duk irin jawabai da shugabannin za su yi na siyasa su dubba wannan batu, kuma ba zamu iya samun biyan bukata ba ai da tallafin shugabanin saboda su ne masu wuka da nama. Kuma irin kokarin da matasan suke da shi da kuma niya na daukar makomarsu da kansu dole sai masu ruwa da tsaki sun saka baki."

Matasa maza da mata, da shugabannin kamfanoni da na sauran kungiyoyi masu zuba jari za su kasance a wannan taro wanda shugabannin kasashe kusan 30 daga kasahen Afrika da Faransa za su halarta a birnin Bamako na kasar Mali wanda zai mayar da hankali a game da batutuwa da ke ci-wa najhiyar tuwo a kwa kamar batun tsaro da zaman lafiya da kuma tatalin arziki. Wannan taro na kasahen Afirka da Faransa karo na 27 shi ne kuma karo na biyu da ake yi a Mali tun bayan wanda aka yi na shekara ta 2005.