1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maniyyata sun fara aikin hajjin bana

Ibrahim SaniDecember 17, 2007
https://p.dw.com/p/CcW1

Maniyya kusan miliyan biyu ne ke gudanar da aikin hajjin bana a wannan shekara. Da jijjiɓin safiyar yau ne maniyyatan su ka fita izuwa Minna, don fara wannan gagarumin aiki. Tuni dai Mahukuntan Saudiya su ka ɗauki tsauraran matakan tsaro. Ministan cikin gida na Saudiya, Yarima Nayef bin Abdulaziz, ya ce an ɗauki matakan ne don kare lafiyar maniyya, a lokacin gudanar da aikin hajjin. A gobe talata ake sa ran hawa dutsen arfa, dake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan aikin hajji. Washe gari kuma laraba a cewar rahotanni, a gudanar da idin babbar Sallah.