1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin Jamus dangane da Afurka

October 11, 2007

A wani taro na yini biyu a Berlin kwararru sun tattauna akan makomar manufofin Jamus dangane da Afurka

https://p.dw.com/p/BtuO

Dukkan mahalarta taron da suka hada da ‘yan siyasa da kwararrun masana al’amuran tsaro da ‘yan kasuwa su 15 da kuma ‘yan kallo sun hakikance cewar duk wanda yayi bitar al’amuran Afurka dalla-dalla zai ga cewar daidai take da sauran sassa na duniya kuma matsalolin kasashenta sun banbanta da juna, a saboda haka ba za a iya cewar dukkan kasashen nahiyar su 53 jirgi daya ne ke dauke da su ba. Ta la’akari da haka ya zama wajibi ita ma Jamus ta sauya salon tunaninta a game da nahiyar Afurka in ji Stefan Mair darektar cibiyar nazarin al’amuran siyasa da kimiyya dake birnin Berlin. Ya ce ba zata yiwu dangantaka da Afurka ta ta’allaka da manufofin taimakon raya kasa kawai ba. Wajibi ne dangantakar ta hada da matsaloli na tsaro da tattalin arziki da sauran batutuwa na raya kasa. Mair ya kara da cewar:

“Dukkan tunaninmu da nahiyar Afurka ya danganci taimakon raya kasa ne kawai, amma ba mu taba tsayawa muka yi tunani a game da ko shin matsalolin nahiyar ta Afurka ta shafe mu kai tsaye ba. Kazalika ba mu da wata kasa da muke kawance da ita a manufofin kare kewayen dan-Adam da matsaloli na tsaro dake addabar sassan duniya daban-daban a nahiyar ta Afurka. A saboda haka ya zama wajibi mu dasa wani sabon tubalin kawance da nahiyar Afurka.”

Wannan maganar ta jibanci kawance ne tsakani da Allah. Muddin kasashen Turai na fatan cimma nasara a manufofinsu dangane da nahiyar Afurka to kuwa wajibi ne su kulla huldodi na kawance da su. Tun a shekara ta 2003 kasashen Afurka suka lashi takobin daukar kaddararsu a hannunsu ta gabatar da shugabanci na gari tare da bitar manufofin kowace kasa da kuma irin ci gaban da ta samu a karkashin tsarin APRM. Kasar Ghana ita ce ta farko da aka fara yin wannan gwaji kanta. An saurara daga bakin Samuel Kwasi Adjepong shugaban sakatariyar APRM bangaren kasar Ghana yayi bayani game da haka yana mai cewar:

“Wannan wata sabuwar alkibla ce da shuagabannin Afurka suka fuskanta wanda kuma ke yin nuni da kyakkyawar niyyar dake zukatansu. Wani muhimmin abu game da wannan batu shi ne kasancewar su kansu kasashen Afurka ne suka kikiro wannan sabuwar manufa suke kuma tafiyar da ita daidai yadda ya kamata ba tare da shisshigi daga ketare ba.Su kansu kasashen Afurka ke bita domin su gano wuraren da suke da gibi.”