1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manya na kokarin magance barazanar tsaro a Najeriya

January 5, 2018

Manyan mahukuntan Najeriya sun tashi tsaye da nufin maganta rigingimun kabilanci da na addini da ke kara ta'azzara a kasar, matsalolin da ga alamu ke rikidewa daga zamantakewa ya zuwa batu na siyasa.

https://p.dw.com/p/2qPj4
Äthiopien Gipfel Afrikanische Union - Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da babban sufetan ‘yan sandan kasar sun share tsawon wunin Juma'a suna nazarin mafitar rikicin da ya kama hanyar rikidewa ya zuwa batu na siyasa. Kama daga jihar Ribas ya zuwa Kaduna sannan a baya-bayan nan jihar Benue dai sannu a hankali  batun tsaro da zaman lafiya na neman kubuce wa gwamnatin tarrayar Najeriya a halin yanzu.

Anschlag Autobombe in Kaduna Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Asarar sama da mutane 50 a jihar ta Benue da wasu 20 a Omokun Ribas din game da kisan wani sarki a Kaduna dai ya tayar da hankali a Najeriyar da ke kallon rushewa cikin lamuran tsaro cikin kasar mai kara kusantar zabe, abin kuma da ya har ila yau ya dauki hankalin mahukunta na kasar da suka share tsawon kusan sa'o'I uku suna tattaunawa a tsakanin babban sufetan ‘yan sanda na kasar Ibrahim Idris da kuma shugaban kasar ana ganawa da nufin neman mafita.

To sai dai kuma majiyoyi na tsaro dai na ta'allaka sabbin rigingimun da karuwar ayyukan kungiya ta asiri da ke neman mamaye sassan kasar daban-daban, abin kuma da a tunanin Solomon Dalung ministan wasanni da matasa, ya sa da kamar wuya a yi saurin yanke hukunci a bisa jerin rigingimun da ke tayar da jijiyar wuya a halin yanzu.

Bayan kamalla ganawar dai shugaban ‘yan sandan dai ya ce ana shirin tura jami'an ‘yan sanda a daukacin sassan kasar, yana mai tabbatar da cewar tuni aka fara kama masu ruwa da tsaki da jerin rigingimun. Ana dai kallon daukacin rikicin a matsayin gwagwarmayar neman mallakar filaye a tsakanin makiyayan da ke kara yin kudu da kuma manoman da ke ganin barazana ga filayen nasu.

To sai dai koma yaya take shirin kayawa tsakanin jami'an tsaron da dillalan a mutun dai, babban aiki na gwamnatin kasar da ke fuskantar sabon yanayi na siyasa a bana a cikin halin rigingimu iri iri cikin kasar a halin yanzu.