1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manzon Birtaniya a Afghanistan ya yi murabus

September 8, 2010

Manzon Birtaniya a Afghanistan ya yi murabus bayan bata -kashi tsakanin sojojin NATO da na Amirka

https://p.dw.com/p/P77e
Hoto: picture-alliance/dpa

Ofishin kula da harkokin wajen Birtaniya da ke birnin London ya sanar da cewar manzon ƙasar na musamman a ƙasashen Afganistan da kuma Pakistan zai yi murabus ba tare da wani ɓata lokaci ba, biyo bayan taho mu gama tsakanin dakarun ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO da ke yaƙi a Afganistan da kuma dakarun Amirka yayin da suke ƙoƙarin yaƙi da 'yan ƙungiyar Taliban.

A watan Yuni ne dai Sherad Cowper -Coles ya sauka daga muƙaminsa, amma na wucin gadi, inda ofishin kula da harkokin wajen zai sake komawa ga muƙamin. A cikin wata sanarwar da ofishin sakataren kula da harkokin wajen Birtaniya Williams Hague ya fitar, ya ce Sherard ya bayar da gagarumar gudummuwar sa ga manufofin gwamnatin Birtaniya ga Afganistan da kuma Pakistan.

A halin da ake ciki kuma, masana harkokin siyasar ƙasa da ƙasa na faɗin cewar, za'a ci gaba da samun saɓani a tsakanin Amirka da gwamnatin shugaba Hamid Karzai musamman game da salon yaƙi a Afganistan, wanda ke yin sanadiyyar mutuwar fararen hula.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umar Aliyu