1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani a kan kasafin kudi a Nijar

Gazali Abdou TasawaOctober 8, 2014

A Jamhuriyar Nijar bangarorin siyasar kasar sun fara bayyana ra'ayinsu a kan sabon kasafin kudi na shekara ta 2015 da gwamnati ta mika gaban majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/1DSGU
Hoto: DW/M. Kanta

Kasafin kudin kasar da gwamnatin ta gabatar dai ya tasamma sama da biliyan 17 na Cefa, wanda kuma sama da kaso 50 cikin dari na kudin gwamnatin za ta samo su ne daga cikin gida. Sama da miliyan dubu 30 na kudin Cefa ne dai kasafin kudin shekara mai kamawa da gwamnatin ta gabatarwa majalisar dokokin ya haura na wanann shekara ta 2014 da muke ciki.

Gwamnati za ta nemi tallafi daga ketare

Wanann karon dai gwamnatin ta ce zata dogara da tallafin kudi da take samu daga kasashen ketare wanda kudin da ya haura kaso 40 daga cikin 100 kawai, sanann gwamnatin ta ce za ta yi amfani da wadannan kudade domin gudanar da ayyukan gina kasa da kyautata rayuwar al'umma kamar yadda Malam Yahuza Sadisu ministan da ke kula da hulda tsakanin gwamnati da sauran hukumomin Jamhuriyar ta Nijar ya tabbatar.

DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi
Minita Yahouza Sadissou MabobiHoto: DW/M. Kanta

Tabbatar da tsaro da kuma samar da abinci


Haka zalika gwamnatin ta ce a shekarar mai kamawa za ta yi amfani da kudadan wajan gudanar da wasu ayyukan kamar na tabbatar da tsaro dama wasu manyan ayyuka da ke a karkashin tsarin nan na 'yan Nijar su ci da 'yan Nijar da gina hanyar jirgin kasa. Bugu da kari za ta dage wajan biyan kudadan bashi na ciki da na waje. To saidai da ya ke tsokaci akan sabon kasasfin kudin kasar Honnorable Amadu Jibbo na jamiyyar adawa ta UNI cewa ya yi ko a wanann karon ma dai kasafin kudin da gwamnatin ta gabatar masu na neman yin burga ne kawai ba wai dan ana iya aiwatar da shi ba.

Bauarbeiten an der Bahnlinie Niamey-Cotonou
Aikin titin jirgin kasa a NijarHoto: DW/Mahaman Kanta

Yanzu dai takardun kasafin kudin din na hannun 'yan majalisar dokokin wadanda tuni su ka rarraba su ga kwamitocin majalisar daban-daban da za su kwashe sama da wata guda suna nazarin shi kafin sake gabatar da shi ga zauren majalisar domin yin babbar muhawara a kai.