1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Martani kan dokar hana I'tikafi a masallatai

April 14, 2021

Kamar sauran kasashen duniya, al’ummar Musulmi na ci gaba da martani a kan matakin hana sallar I'tikafi da shugabanin addinin musulunci a Najeriya suka dauka don takaita yaduwar corona.

https://p.dw.com/p/3rxGy
Saudi-Arabien Mekka | Gebet mit Social Distancing
Hoto: picture-alliance/abaca/Balkis PRess

A Najeriya kamar sauran kasashen musulmi, mabiya addinin islama a kasar na ci gaba da mayar da martani kan matakin da majalisar koli mai kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta dauka na hana al’ummar musulmi I’tikafi, wannan shi ne karo na biyu da a jere da ake daukar wannan mataki a yayin Azumin watan Ramadana tun bayan bullar annobar corona a watan Disambar shekarar 2019.

Karin Bayani:  Saudiyya: An takaita yawan alhazai bana

Nigeria religiöse Gewalt 2001
Musulmai na baiyana takaici kan rashin walwala a gudanar da ibadaHoto: AP

To ita dai majalisar koli a kan harkokin addinin musulunci a Najeriyar, ta fitar da wata sanarwa ce a shafinta na Twitter inda ta bukaci al’ummar musulmi da su mutunta dokokin kare yaduwar cutar  Corona a yayin wannan azumin wata na Ramadana. Yayin da sanarwar ta ci gaba da cewa haramcin gudanar da itikaf na nan daram, kazalika kuma a guji gudanar da tarukka a wannan lokaci da ake gudanar da wannan ibada ta watan Ramadan. Karin Bayani:  Coronavirus: Babu taba Ka'aba a hajjin bana

Ramadan 2020 Ägypten Kairo Gebet al-Azhar-Moschee
Kasashen musulmi na mutunta dokar saka tazara a yayin ibadaHoto: SAMER ABDALLAH/AFP/Getty Images

Wannan dama ba shi bane karon farko da ake sanya wannan dokar, ko a azumin shekarar da ta gabata an samu dakatar da irin wadannan ibadu na itikaf da kuma sauran salloli na Tarawihi daga hukumomi, a kokarin da suke cewa suna yi na kawar da yaduwar cutar Covid 19. Tuni wasu malamai suka soma nuna ‘yar yatsa da kuma cewa da sake ga wannan mataki na haramcin itikaf da majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ta yi, musammam a irin wannan lokaci da Najeriya ke neman taimako daga Allah don magance matsalolin tsaro da talauci da suka addabi kasar. Karin Bayani:  Najeriya na fafutukar yaki da ta'addanci

Duk da irin wannan mataki da hukumomi suke dauka don takaita yaduwar wannan cuta ta Corona, to har yanzu ba kasafai ake ganin jama'a na bin wadannan matakan kariyar ba, in ban da wuraren da dokar ta zama tilas, matukar mutum na son kai ziyara wuraren da aka tabbatar da dokar ta hana yaduwar corona. Baya dai ga Najeriya ma, akwai wasu kasashen musulmi da dama da suka sanya dokar hana jam'i da itikaf, Saudiya  ce kasa ta farko da ta soma daukar matakin a duniya.