1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin ƙasashen duniya a kan Isra'ila

Knipp, Kersten/MNAJune 10, 2016

Majalisar Ɗinkin Duniya ta soki matakin da rundunar sojan Isra'ila ta ɗauka na hana Falasɗinawa izinin shiga Gabar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/1J4a2
Golanhöhen israelischer Ministerpräsident Benjamin Netanjahu
Benjamin Netanjahu firaministan Isra'ilaHoto: Getty Images/AFP/S. Scheiner

Majalisar Ɗikin Duniya ta soki matakin da rundunar sojan Isra'ila ta ɗauka na hana Falasɗinawa izinin shiga cikin Isra'ila biyo bayan mummunan harin da aka kai a birnin Tel Aviv, da cewar jan kunne dukkan al'ummar Falasɗinu ne. Bayan da a ranar Laraba wasu 'yan bindigar Falasɗinu sun harbe Isra'ilawa huɗu har lahira an rufe dukkan hanyoyin da ke shiga Isra'ilan daga Gabar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza, amma za a kyale marasa lafiya da masu neman taimakon jin kai shiga Isra'ila.

Sanarwar MDD ta yi suka a kan matakin na Isra'ila

Wata sanarwa da ofishin shugaban Hukumar kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Zeid Ra'ad Al Hussein ya fitar, ta yi tir da harin da aka kai a birnin na Tel Aviv amma a lokaci guda ta nuna damuwa da wannan martani da Isra'ila ta mayar na hana Falasɗinawa izinin shiga ƙasar da cewar jan kunnen dukkan Falasɗinu ne matakin kuma da ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa.

Schweiz UN-Menschenrechtsrat Said Raad al-Hussein
Zaid Raad al-Hussein Shugaban Hukumar kare hakkin dan Adam na MDDHoto: picture-alliance/dpa/M. Trezzini

Isra'ila ta ce ta ɗauki matakan kariya ne saboda kariya daga hare-hare na ta'addanci

Sai dai a lokacin da take mayar da martani na wannan sukar, Isra'ila ta kare matakanta da cewar matakai ne halattattu ta dauka da nufin kare 'ya'yanta daga 'yan ta'adda.Da ma jin kadan bayan kai harin da yayi sanadin rayukan Isra'ilawa huɗu a birnin na Tel Aviv da ke gabar teku, Firaministan Benjamin Netanyahu ya ce za a ɗauki matakan da suka dace bisa munafar kare ƙasar Isra'ila.

Israel Anschlag in Tel Aviv
Hoto: Getty Images/AFP/G. Markowicz

Ya ce: "Ina ganin an hana aukuwar wani babban bala'i sakamakon bajintar da mutane da jami'an tsaro da kuma 'yan sanda suka nuna. Za mu dauki matakan da suka dace na farma maharan tare da kare wadanda ke bukatar kariya."

Tun a cikin watan Oktoban bara Isra'ila ke fama da sabbin hare-hare da kawo yanzu suka yi sanadin mutuwar Isra'ilawa 32 da Falasɗinawa fiye da 200 da baki 'yan kasashen waje huɗu ciki har da Amirkawa biyu.