1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Amurka akan sanarwar mallakar makaman nukiliya daga Koriya Ta Arewa

February 10, 2005

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta ce kasar a shirye take ta fuskanci duk wata barazanar da ka ta so daga Koriya ta Arewa

https://p.dw.com/p/BvdD
Condoleeza Rice a Luxemburg
Condoleeza Rice a LuxemburgHoto: AP

A lokacin da take mayar da martani akan sanarwar da ta zo ba zato ba tsammani daga Koriya ta Arewa cewar kasar na mallakar makaman nukiliya kuma zata janye daga zaman tattaunawar da ake yi akan shirye-shiryenta na kera wadannan makamai, sakatariyar harkokin wajen Amurka dake kammala ziyararta ta tsawon mako guda ga kasashen Turai da Yankin Gabas ta Tsakiya, Condoleeza Rice ta ce fadar mulki ta White House na shawartawa da kawayenta akan matakan da zasu iya dauka akan kasar Koriya ta Arewar nan gaba. Ta ce Amurka da kawayenta a shirye suke su tinkari duk wata barazanar da ka taso daga kasar koriya ta Arewa, wacce ke daya daga cikin jerin kasashen da shugaba Bush ya musulta su tamkar shaidanun kasashe. Sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta nanata yin kira ga kasar Koriya ta Arewar da ta koma kan teburin tattaunawar domin kuwa al’umarta ne zasu fi fama da radadin matakan da za a dauka na kara mayar da ita saniyar ware, in har ta ci gaba da nuna taurin kai. Wannan sanarwar da ta zo a ba zata daga Koriya ta Arewa ta sanya murna ta kara komawa ciki a kokarin da Amurka da kasashen Turai ke yi na hana yaduwar muggan makaman kare dangi da kuma gurbataccen yanayin da ake fama da shi a shawarwarin da ake yi akan shirye-shiryen mallakar wadannan makamai da kasar Iran ke yi. Condoleeza Rice ta fada wa taron manema labarai a Luxemburg cewar kasar Amurka tun a cikin shekaru na 1990 ne take tattare da imanin cewar kasar koriya ta Arewa na shirin kera makaman nukiliya, amma ba ta tantance ranar da kasar zata fito da maganar a fili ba, har sai ya zuwa yau alhamis. A dai halin da ake ciki yanzun ita Amurka bata da wata niyya ta daukar matakai na soja akan Koriya ta Arewa ko Iran, amma zata ci gaba da nazarin sauran matakai na takunkumin da zata iya kakaba wa kasashen biyu, a maimakon haka ma ita Amurka ta tsayar da shawarar janye sojojinta dubu 37 daga Koriya ta Kudu, wanda ya kama kashi daya bisa uku na yawan sojojin da ta tsugunar a wannan yanki. Fadar mulkin Koriya ta Arewa ta fito karara da bayyana cewar ba zata ci gaba da halartar zauren shawarwarin shirinta na nukiliya ba, kuma tuni ta kera isassun bamabaman da zata iya kare kanta daga duk wani harin da Amurka zata kai mata. Wannan sanarwar ta zo daidai lokacin da ake faman neman bakin zaren warware matsalar nukiliyar kasar Iran, wacce ta dabaibaye yanayin ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta kawo nahiyar Turai. Condoleeza Rice ta musunta zargin da ake yi na cewar Amurka na magana ne da baki biyu-biyu a game da kasashen na Iran da Koriya ta Arewa ta kuma samu goyan baya akan haka daga kawayenta kasashen Turai.