1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Boko Haram kan shirin yi mata afuwa

April 10, 2013

Shugaban Kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lidda’awati Wal Jihad ko kuma Boko Haram ya shure kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi na yi wa 'yayansa afuwa inda ya ce ba su yi laifin komai ba balle a ce za’a yi musu afuwa.

https://p.dw.com/p/18DlK
Hoto: AP

Cikin wani sakon na bidiyo da Kungiyar ta fitar mai tsawon mintuna 30, Shugabanta Imam Abu Muhammad Abubakar Ibn Muhammad Shekau yayi Magana cikin harsunan Hausa da Larabci da kuma surka turanci, inda ya ce sune ma aka yi wa laifi saboda haka in ma yin afuwa ne sune ya kamata a ce za su yi, amma kuma ba su shirya yi ba. Shugaban Boko Haram ya kuma nemi al'ummar musulmi da su daina bin tsarin mulkin da ba na Allah ba, idai suna son makoma mai kyau a ranar gobe kiyama.

Nigeria Kano Bombenanschlag
Hara haren da Boko Haram ke kaiwa na lamshe rayuka da dukiyoyi.Hoto: Reuters

Ya kuma ce sune ke da alhakin kona makarantun Boko kuma zasu ci gaba da kai hare-hare kan muradan gwamnatin da ke amfani da jami'an tsaronta wajen yaki da su. Imam Abubakar Shekau ya kuma jaddada kudirin Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da gwagwarmaya don kafa shari'ar musulunci a tarayyar Najeriya inda ya ce ba gudu ba ja baya a wannan fafutukar ko da kuwa za'a karar da su.

Ina aka kwana game da sulhu a Najeriya?

Babu shakka wannan matsayi na kungiyar ba zai yi wa duk wani mai ganin an kawo karshen wannan tashe-tashen hankula dadi ba musamman ganin yadda aka sa rai kan wannan shirin na yin afuwa domin yin sulhu da Kungiyar. Sai dai wasu ‘yan kasar kamar malam Hamza Umar Usman na ganin jinkirin da gwamnatin tarayyar Najeriya tayi na karbar shawarwarin da aka bata tun farko shine ya haifar da wannan matsalar. To amma wasu kamar Muhammad Bello Sarkin Arewan Bolari wani malami a Jami'ar jihar Gombe na ganin tun farko ma gwamnatin ba ta dauko hanyar yin wannan afuwa don yin sulhu da gaskiya ba, ganin yadda ake ci gana da farautar ‘yan kungiyar ta Boko Haram. Sai dai kuma da dama suna ganin akwai fatar cimma nasarar yin sulhun idan dukkanin bangarorin zasu kai zuciya nesa.

Nigeria Abuja Notstand
Matakn soje da shugaba Jonathan ke dauka ba sa magance matsalar tsaroHoto: picture-alliance/dpa

Shwarwari kan hanyoyin afuwa ga Boko Haram

Wannan sako dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al'ummar Najeriya ke dakon rahoton da kwamitin da gwamnatin kasar ta kafa wanda zai ba ta shawara kan hanyoyin da za'a bi don yin afuwar ga 'yan Boko Haram. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin da ma kwamitin ba su ce komai ba kan wannan sabon faifai da kungiyar gwagwarmayar ta fitar, wanda da dama ke kallon sa a matsayin mai mai da hannun agogo baya a kokarin kashe wutar tahse-tahsen hankulan da ya gurgunta al'amuran musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Rahotanni cikin sauti na kasa

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe