1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Turai kan kalaman Trump

January 17, 2017

Shugaban Amirka mai jiran gado a wata hira da ya yi da mujallar Bild ta Jamus, ya jaddada ikirarinsa a lokacin zabe na janye kasarsa daga kungiyar kawancen tsaro ta NATO, ya na mai cewa kungiyar ba ta wani alfanu

https://p.dw.com/p/2VvGF
US Präsident Donald Trump
Hoto: picture-alliance/Photoshot

 Wadannan kalamai dai sun haifar da damuwa da kuma ayar tambaya daga masharhanta da dama a cikin kungiyar ta NATO da kuma kungiyar tarayyar Turai. Abdullahi Tanko bala na dauke da karin bayaani a cikin wannan rahoton da ya hada mana.

Trump wanda ke zama tamkar mazari ba'a san inda ka sa gaba ba, an jima ana nuna damuwa game da matsayinsa a kan kungiyar NATO. Ko da yake shugabanin soji a rundunar kawancen tsaron sun yi kokari a 'yan makonnin da suka wuce na tabbatar da yarda da amincin shugaban na Amirka a kan kungiyar, inda a karshen shekarar da ta gabata, babban sakataren kungiyar kawancen tsaron Jens Stoltenberg ya ce Trump ma'aboci ne ga NATO.

To sai dai kuma a yanzu alamu na nuna rashin tabbas na kara baiyana inda Trump ya baiyana NATO da cewa ta zama tsohuwar yayi wadda ta wuce zamaninta kamar yadda ya baiyana a hirar da ya yi da mujallar Bild.

Ko da aka tambaye shi game da wannan batu ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya yi tsokaci yana mai cewa:

" Dawowa ta kenan daga wata tattaunawa da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, inda babu shakka aka tabo batun da shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump

 ya yi cewa wai NATO ta zama tsohuwar yayi."

Ministan harkokin waje na Jamus Steinmeier
Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier Hoto: Reuters/B. Tessier

Kwararru da masharhanta dai na baiyana damuwa game da makomar wadannan kalamai da kuma inda suka dosa. Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier har ila yau da yake magana a Brussels ya ce, an ji banbancin ra'ayi a irin kalaman da wasu ministoci da Trump ya nada suka yi yayin tantance su a majalisar dokoki.

" A irin kalaman da muka ji da suka gabata daga wanda aka nada ministan tsaron Amirka yayin tantance shi a Washington a kwanakin da suka gabata an sami banbanci ra'ayi kan wannan matsayi. A saboda haka za mu jira mu gani abin da zai biyo baya game da manufofin Amirka."

Shi dai Trump a hirar da ya yi da mujallar ta Bild ya yi kakkausar suka guda biyu ga kungiyar ta NATO. Na farko ya ce kungiyar ba ta yin wani abin a zo a gani wajen yaki da ta'addanci. Sannan

na biyu, mambobin kasashe basa biyan nasu kason kudin da ya dace na tafiyar da kungiyar inda ake barin nauyi a kan Amirka wanda wannan rashin adalci ne.

Wannan dai hakki ne da ya rataya a wuyan baban sakataren kungiyar ta NATO da ya tattauna da Trump.

Trump dai ya zama tamkar mazari ne da ba'a san inda ya sa gaba ba.

Ministan harkokin wajen Luxemburg Jean Asselborn
Ministan harkokin wajen Luxemburg Asselborn Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

A nasa bangaren Ministan harkokin wajen Luxemburg Jean Asselborn, ya yi tsokaci ne kan yarjejeniyar cinikayya tsakanin Turai da Amirka wanda shima Trump ya sanya shakku a akan sa.

" Zai kasance abin kaico idan Amirka wadda ke daukar kanta a matsayin babbar kasar dimokradiyya a duniya ta amince da daukar wannan mataki."

Trump dai ya tada kaimi ne na masu ra'ayin hannun riga da kungiyar Tarayyar Turai, kamar yadda ya kasance ga rajin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU. A waje guda kuma ya farkar da kungiyar tarayyar Turai ta sake yin duba ga lamuranta.