1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunta masu kara aure a boye a Masar

Mahamud Yaya Azare LMJ
November 30, 2021

Dokar hukunta mazajen da ke yi wa matansu kishiya ba tare da sanin matan ba, na ci gaba da jawo cece kuce a Masar.

https://p.dw.com/p/43fex
Zeichnung Polygamie im Iran
Hukuncin ga mazan da suka kara aure ba tare da sanin matansu ba a MasarHoto: fararu.com

A yayin da wasu ke ganin dokar za ta taimaka wajen kare mata da iyali, wasu kuwa na ganin cewa dokar za ta bude kofar barna ne da aikata alfasha cikin al'umma. Dokar ta tanadi daurin watanni shida da cin tarar kudi fam dubu 50 na kudin kasar Masar, wanda ya kama kimanin Naira miliyan biyu. Majalisar dokokin kasar ta amince da daftarin dokar ne domin kare zamantakewar iyali da hana kunsawa mata bakin ciki, inji Najla Mustapha da ke zaman guda daga cikin 'yan majalisar da suka gabatar da kudirin dokar da aka aminta da shi.

Farida Rustum daya daga cikin masu fafutukar kwatar 'yancin mata, na daga cikin masu ganin an yi matukar sassauci a hukuncin wannan dokar. To sai dai a hannu guda cibiyar binciken addinin Musulumci ta Al-azhar ta ce, dokar karan tsaye ne ga tafarkin shari'a. Itama Dakta Isra'a Budair malama a tsangayar ilimin zamantakewa a jami'ar Alqahirah, tana ganin an yi baya ba zani a wannan dokar. Galibin matan kasar ta Masar na yin lale maraba da wannan doka da suka tabbatar da cewa, duk da ba za ta hana yi musu kishiya ba za ta dan rage musu takaici.