1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta karfafa matakan tsaro a Sinai

October 29, 2014

Masar ta fara gina shinge tsakaninta da yankin zirin Gaza

https://p.dw.com/p/1De19
Hoto: picture-alliance/landov/Abed Rahim Khatib

Gwamnatin kasar Masar ta fara gina shinge a kan iyakar kasar da yankin zirin Gaza na Falasdinawa, domin kare shigar tsageru da ke kai hari wa jami'an tsaron kasar ta Masar. Ana sa ran saka shinge mai tsawon mita 500 cikin yanki mai nisan kilomita 10 da ke iyakar.

Matakin ya biyo bayan hallaka kimanin sojoji 30 a yankin Sinai. Tuni mahukuntan kasar suka saka dokar ta baci na tsawon watanni uku a yankin arewacin Sinai, domin daukan matakan dikile hare-haren da ake samu. Shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah al-Sisi ya zargi baki da kai hare-hare wa jami'an tsaron kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe