1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki ma'aikacin Al-Jazira dayaa Masar

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 1, 2015

Shugaban kasar Abdel Fatah al-Sisi ya ba da umurnin sallamar daya daga cikin ma'aikatan gidan talabijin din Al Jazeera Peter Greste tare da tisa keyarsa zuwa Ostareliya.

https://p.dw.com/p/1EUBY
Hoto: REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper

Rahotannin sun tabbatar da cewa tuni Greste ya bar birnin Alkahira na kasar ta Masar zuwa Ostareliya da ke zaman kasarsa ta asali bayan da ya kwashe tsahon kwanaki 400 a gidan kaso

Ma'aikatan gidan talabijin na Al Jazeera uku ne da suka hadar da Peter Greste da Mohamed Fahmy da ke da shaidar zama dan kasar Kanada da kuma Masar sai Baher Mohamed dan kasar ta Masar suke tsare a gidan kaso a Masar sakamakon samunsu da laifin yada labaran karya da kuma goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da gwamnatin kasar ta haramta, wanda kotun kasar ta ce ta yi kana ta yanke musu hukuncin shekaru 10 a gidan kaso.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar a saki Mohamed Fahmy nan da 'yan kwanaki, sai dai babu karin bayani dangane da makomar Baher Mohamed da ke zama dan asalin kasar ta Masar.