1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta tsoshe kafofin Internet 60

Abdul-raheem Hassan
June 12, 2017

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama, sun tabbatar da katse shafukan yada labarai ta kafofin yanar gizo akalla 60 da Masar ta yi, matakin ya kuma shafi sauran cibiyoyi da ke samar da interent a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/2eYun
Entwicklung der Unruhen in Ägypten Flash-Galerie
Hoto: dapd

A tun karshen watan Mayu da ta gabata ne hukumomin kasar suka fara toshe kafofin yada labarai ta Internet na aksashen waje da na cikin gida guda 20. Cikin wadan da abin ya shafa, akwai kamfanin yada labaran kasar Masar mai zaman kanta wato Mada Masr da kuma kamfanin Al-Jazeera reshen ta da ke Masar.

Ana dai zargin wasu shafukan da caccakar manufofin gwamnati da ma sukar ayyukan cin hanci da rashawa a cikin kasar, sai dai kawo yanzu bangaren gwamnati ba su ce komai a kan toshe wadannan kafofin yada labarai ba.

Alkaluman da kungiyar da ke fatutikar kare 'yan jarida a duniya "Reporters without Borders" ta wallafa a wannan shekara, na nuna kasar Masar a jerin kasashe na 161 cikin kasashen 180 dake mutunta 'yancin albarkacin baki a fadin duniya.