1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar tana ci gaba da kai farmaki kan tsageru a Libiya

Suleiman BabayoFebruary 16, 2015

An fara mayar da martani kan hare-haren da Masar ta kaddamar da mayaka masu neman kafa daular Islama a kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/1EcP7
Ägypten Reaktion auf Ermordung koptischer Christen durch IS
Hoto: imago/Xinhua

Kasar Hadaddiyar Daular Laraba ta bai wa kasar Masar goyon baya bisa hare-haren da ta kaddamar kan kungiyar neman kafa daular Islama ta kasar Libiya, bayan mayakan kungiyar sun hallaka 'yan kasar ta Masar 21 Kiristoci mabiya darikar Coptik.

A wannan Litinin rahotanni sun nuna cewa jiragen saman yakin kasar ta Masar sun ci gaba da luguden wuta kan wuraren da ake zargin mayakan da suka hallaka 'yan Masar suna buya. Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya nuna bakin-ciki da kisan da aka yi wa 'yan kasar ta Masar. Tuni mahukuntan Masar suka nemi kawancen da Amirka ke jagoranta da suka kai farmaki kan mayakan IS na Libiya.