1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masifar mahaukaciyar guguwar Wilma a kudancin Amirka

October 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvOI
Mahaukaciyar guguwar Wilma ta yiwa yankin tsibirin Yucatan na kasar Mexiko kaca-kaca. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce cikin sa´o´i kalilan guguwar ta yi daya-daya da wannan yanki. An kafa dokar ta baci a yankuna da dama na kasar, musamman wuraren da ruwa ya malale a birnin Cancun, yayin da kuma ´yan sanda suka kame mutane da dama masu kwasar ganima. Ita ma cibiyar ´yan yawon shakatawa ta Playa del Carmen ta yi kaca-kaca. Hukumomin sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 3 a Yucatan da kuma tsibirin Cozumel dake kusa. Tun gabanin karatowar guguwar ta Wilma aka kwashe ´yan yawon shakatawa kimanin dubu 30 daga yankin zuwa tudun mun tsira. Masu hasashen yanayi na sa ran cewa nan ba da dadewa ba guguwar zata doshi jihar Florida da kasar Kuba.