1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masifar wutar daji a kudancin jihar California ta ƙasar Amirka

October 24, 2007
https://p.dw.com/p/C15j

Har yanzu ba´a shawo kan wutar daji dake ci a kudancin jihar California ta kasar Amirka ba. Iska mai karfi hade da zafin rana na kawo cikas ga aikin kashe wannan gobara wadda ta kasance wani bala´i na gobara mafi muni a tarihin Amirka. Yanzu haka dai an kwashe mutane kimanin miliyan daya musamman a yankin San Diego daga gidajensu. Bruce Cartelli na ma´aikatar kashe gobara ta jihjar California ya bayyana halin da ake ciki yana mai cewa.

Cartelli:

“Abin yayi muni. An yi asarar dubun dubatan gidaje yayin da wasu daruruwa suka lalace. Alal hakika wannan dai shi ne abu mafi muni da na taba gani a cikin shekaru 36 na wannan aiki.”

A gobe alhamis shugaban Amirka GWB zai kai ziyara a yankin da wannan bala´i ya afkama.