1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu cutar Ebola na samun sauƙi a Najeriya

August 11, 2014

A karon farko mahukunta kula da lafiya sun bayyana cewar mutane takwas da suka kamu da Ebola na samun sauƙi ta yadda za’a iya sallamar wasu daga cikinsu daga asibiti.

https://p.dw.com/p/1CsW6
Afrika Symbolbild Ebola
Hoto: AFP/Getty Images

Bayyanan da ministan kula da lafiya Najeriya ya yi a game da zahirin halin da ake ciki a kan wannan mummunan cuta ta Ebola, ya nuna cewar ya zuwa yanzu an samu ƙaruwar yawan mutanen da suka yi cuɗanya da ɗan ƙasar Liberiyan da ya shigo da cutar a Najeriya watau Patrick Sawyer. Dokta Abdussalam Nasidi shi ne daraktan cibiyar kula da kare cututtuka a ma'aikatar lafiya ta Najeriya.

‘'Daga cikin mutane takwas da muke da su a asibiti biyar sun kusan warkewa sauran guda uku ne kawai muke ƙoƙarin muga Allah ya sa sun rayu, amma yanzu haka muna da mutane 187 waɗanda muka tabbatar sun yi cuɗanya da marigayi Sawyer.''

Hukumomin Najeriya na yin shawarwari da ƙasashen maƙwaɓta domin daƙile cutar

Najeriyar dai ta ce ta fara tuntuɓar ƙasashen da take maƙwaɓtaka da su irin su Jamhuriyar Nijar da Benin da kuma Kamaru don ɗaukan matakai na bai ɗaya na daƙile yaɗuwar cutar. Minstan ƙasa na kula da lafiya Dokta Halliru Alhassan ya bayyana matakan da Najeriyar ta ɗauka ta kai ga samun nasara a kan mutanen da suka kamu da cutar su takwas kwanaki 22 bayan kamuwarsu abin da ya jefa sabuwar fata.

Ebola Liberia 06.08.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

‘'Wannan cuta da yawan kwanakin da take yi a cikin mutum, wanda ya tashi daga kwanaki biyu zuwa 21, a yanzu kwanaki 22 da waɗannan mutane da suka kamu cutar na jikinsu, kuma ana kula da su waɗanda za'a iya sallamarsu domin ci gaba da kulawa da su.''

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane