1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu gwagwarmayar jihadi sun kame birane a Iraki

June 11, 2014

Dakarun Iraki sun shiga cikin shirin ko ta kwana a fadin kasar, biyo bayan mamayar da 'yan jihadi da 'yan bindigar kabilu suka yi wa sassa daban-daban a gabacin kasar.

https://p.dw.com/p/1CGYc
Bewaffnete Sunniten in Falludscha
Hoto: picture-alliance/dpa

A wani ba zata da mayakan sa kan kungiyar Da'ish da ke gwagwarmayar kafa shari'ar musulunci a kasar Iraki da kewaye suka yi, cikin kankanin lokaci sun yi nasarar mamaye birnin Mosul, na biyu a girma a kasar, da kuma biranen Nainawa da Salahdden. Mayakan sun kuma mamaye rijiyoyin mai da ke garin Beji kusa da birnin Bagadaza. Sannan an ga yadda dakarun sojin gwamnati ke rantawa a na kare daga yankunan, sannan an kuma ga yadda motocinsu masu sulke da kuma barikokin soji da ofisoshin 'yan sanda na cin wuta.

Irak Anschläge Nuri al-Maliki 12. Dez. 2011
Hoto: Getty Images

An kuma sako wadanda ke daure a gidajen yari, lamarin da ya sanya Firaministan Irakin Nuri al-Maliki, wanda ke fuskantar gagarumar adawa daga jam'iyyun 'yan Sunni da Kurdawa, ya nemi majalisar dokokin kasar ta bashi damar sanya dokar tabaci a kasar.

"Hatsarin da ke fuskantar lamarin tsaro, zai tilasta mana daukar matakan gaggawa don tunkarar 'yan ta'adda da kare talakawa. Don haka muke kira ga majalisa da ta bamu damar sanya dokar tabaci ba da wata wata ba da kuma daukar matakan ba sani ba sabo."

Sakacin jagororin dakarun gwamnati

Usamal Najfi shugaban majalisar dokokin ta Iraki, ya dora laifin mamayar da 'yan bindigar suka yi a yankuna da dama kan sakacin jagororin dakarun gwamnati.

"Wannan abu ya faru ne sakamakon saken jagororin dakarun gwamnati. An basu duk bayanan asiran da suka wajaba, kan yunkurin da 'yan ta'adda ke yi. Amma suka kasa daukar matakan riga-kafi."

Kasar Amirka da ta yaki kasar kuma ta kawar da Saddam Hussein kana a yanzu take goyan bayan Nuri al-Maliki, ta sha alwashin taimaka masa ya murkushe wadanda ta kira birbishin Alka'ida.

Irakische Flüchtlinge im Irak
Hoto: picture-alliance/AA

Makarkashiya daga Amirka

Shi kuwa Sheik Abdul Hakem Sa'adi, daya daga cikin shuwagabannin kabilun kasar danganta abin da ke faruwa yayi da makarkashiyar da kasar Amirka ta dasa a kasar a yayin mamayar da tayi wa Iraki.

"Bayan mamayar da Amirka da Birtaniya suka yi wa Iraki, sun yi amfani da tsarin fasasu ka kama, ta hanyar gwara kan kabilu da basu makamai don su kare kansu daga juna. Lamarin ya ba wa Nuri al-Maliki damar kafa kungiyoyin 'yan banga da sunan dakarun sojin Iraki, wadanda basu da aiki face bibiyan 'yan adawa da kakkashesu, don ba wa kasar da 'yan bindiga da ke da alaka da ita damar mike kafa a yankin."

Tuni dai dubban mazauna yankunan da ake rikicin suke ta kaurace wa gidajensu.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal