1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu tayar da kayar baya a kudanci da arewacin Najeriya

April 12, 2013

Rikicin 'yan kungiyar Boko Haram da na 'yan bindiga sun mamaye wa'adin mulkin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.

https://p.dw.com/p/18EpB
epa03046192 (FILE) A file photograph Nigerian president Goodluck Jonathan (2-L) standing on the back of a vehicle as he is driven after he was sworn in as president during a ceremony in Abuja, Nigeria 29 May 2011. Media reports state on 31 December 2011 that President Goodluck Jonathan has declared a state of emergency in areas affected by attacks from the Islamist group Boko Haram. Borders will be temporarily closed in the north-eastern states of Yobe and Borno, and central state of Plateau. EPA/STR *** Local Caption *** 00000402757844
Hoto: picture-alliance/dpa

Jama'a barkanku da warhaka. Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan mako ta mayar da hankali a kan tarayyar Najeriya tana mai cewa shugaba Goodluck Jonathan na cikin wani hali na tsaka mai wuya, sannan sai ta ci-gaba kamar haka.

"Yakin da ake yi da masu kaifin kishin addini a arewacin Najeriya ya mamaye wa'adin shugabancin Goodluck Jonathan. Amma bayan harin da kungiyar 'yan tawayen MEND a yankin Niger Delta ta kai da yayi sanadiyar mutuwar jami'an tsaro 12, shugaban na fuskantar barazanar tinkarar sabon rikici a yankin mai arzikin man fetir dake kudancin Najeriya. Tun da farko dai kungiyar ta yi barazanar kai hare hare a matsayin martani ga hukuncin daurin shekaru da yawa da wata kotu a Afirka ta Kudu ta yi wa jagoranta Henry Okah, sai dai da farko hukumomin Najeriya sun bayyana wannan barazana ta kungiyar da cewa fatar baka ce. Kazalika bayan harin hukumomin na Najeriya sun yi kokarin kwantar da hankulan jama'a suna masu cewa kungiyoyin 'yan binga ne tsakankaninsu suka fafata. Sai dai a cewar jaridar abin da ke a fili shi ne bisa ga dukkan alamu gwamnatin Najeriya ta rasa yadda za ta bullo wa rikice rikicen na masu ta da kayar baya a cikin kasar, abin da jam'iyun adawa suka kwatanta da gazawar gwamnatin shugaba Jonatahn."

Zaman dardar a gabaci da tsakiyar Afira

Juyin mulki a Bangui ya janyo kace-nace a biranen Kinshasa da Pretoria, yayin da dakarun Afirka ta Kudu da suka sha kashi a hannun 'yan tawaye a Bangui, yanzu sun kafa sansani a arewacin Kongo, inji jaridar die Tageszeitung.

Chadian soldiers wait on a truck near the Damara, the last strategic town between the rebels from the SELEKA coalition and the country's capital Bangui, on January 2, 2013, as the regional African force FOMAC's commander warned rebels against trying to take the town, saying it would 'amount to a declaration of war.' The rebels, who began their campaign a month ago and have taken several key towns and cities, have accused Central African Republic leader Francois Bozize of failing to honor a 2007 peace deal. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)
Hoto: SIA KAMBOU/AFP/Getty Images

"Har yanzu ba a kawo karshen zaman zullumi a yankin ba da ya samo asali sakamakon juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya., inda yanzu haka mutane dubu 35 suka tsere zuwa jamhuriyar demokradiyyar Kongo tun bayan da 'yan tawayen Seleka suka karbi iko a birnin Bangui bayan sun kifar da gwamnatin shugaba Francois Bozize a ranar 24 ga watan Maris. Su kuma sojojin Afirka ta Kudu da aka tura Bangui don su kare shugaba Bozize, sun tsere zuwa Kongo. Yanzu haka sun mamaye garin Gemena, inda shaidun ganin ido suka rawaito cewa sun mayar da yankin wani sansanin aikin sojin sama. Wasu rahotannin mai sun ce sojojin na Afirka ta Kudu suna aikata ta'asa, abin da wani dan majalisar yankin ya ce ana fuskantar karuwar tabarbarewar tsaro a yankin sakamakon kasancewar sojojin ketare."

Adalci ga kauyawa a Uganda

To zamu kammala ne da jaridar Neues Deutschland wadda ta buga wani labarin mai taken diyya ga mazauna wani kauye a Uganda bayan an kore su.

Ugandischer Bio-Kaffee erfreut sich zunehmender Beliebtheit im In - und Ausland. Copyright: DW/Ludger Schadomsky 07.03.2013, Kampala, Uganda
'Ya'yan gahawa a wata gonar kofi a UgandaHoto: DW/L. Schadomsky

"Hukuncin da wata babbar kotu a Uganda ta yanke, ta samu wani kamfanin gona na Jamus da laifin keta hakkin dan Adam. Fiye da shekaru 11 mazauna wani kauye a kasar Uganda ke gwagwarmayar neman hakkinsu daga kamfanin kula da gonakin gahawa na kamfanin Hamburg Neumann na nan Jamus, bayan an kore su daga yankinsu. Yanzu hakarsu ta cimma ruwa domin babbar kotu a birnin Kampala ta umarci kamfanin da ya biya kyauyawan su kimanin 2000 diyya. Kuma tuni kamfanin yayi lakwarin ba da diyya ta kusan Euro miliyan 11 ga wadannan mutanen."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman